Hare-Haren Boko Haram Ya Sa Mutanen Garin Geidam Sun Fara Tserewa Daga Gidajensu

Hare-Haren Boko Haram Ya Sa Mutanen Garin Geidam Sun Fara Tserewa Daga Gidajensu

- Mazauna garin Geidam sun fara tserewa ganin yadda rikicin Boko Haram ya addabi garin

- An ruwaito cewa, suna tserewa saboda tsoron kada bata-kashi tsakanin sojoji da Boko Haram ya shafesu

- A wani rahoton kuwa 'yan ta'addan sun kai hari wani yankin jihar Borno sun kuma yi kone-kone

Rahotanni daga jihar Yobe sun bayyana cewa mutanen Geidam suna ci gaba da tserewa daga garin sakamakon kutsen da ‘yan Boko Haram suka yi tun ranar Juma’a.

Shaidu sun ce sun tsere ne saboda gudun kada a rutsa da su a bata-kashi da luguden wutar da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram, BBC ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna

Hare-Haren Boko Haram Ya Sa Mutanen Garin Geidam Sun Fara Tserewa Daga Gidajensu
Hare-Haren Boko Haram Ya Sa Mutanen Garin Geidam Sun Fara Tserewa Daga Gidajensu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakazalika, an fafata tsakanin 'yan Boko Haram da sojoji a garin Mainok na jihar Borno mai makwabtaka da jihar ta Yobe, har wasu rahotanni na cewa harin ya rutsa da wasu sojoji da dama.

A baya-bayan nan dai kungiyar ta'addanci ta Boko Haram na zafafa hare-hare a sassa daban-daban na arewa maso gabashin Najeriya, in da suke kone-kone da hallaka sojojin Najeriya.

KU KARANTA: Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna

A wani labari, Wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne sun kona ofishin 'yan sanda na Mainok a ranar Lahadi sakamakon mamayar da maharan suka yi wa sansanin sojoji kafin sojojin Najeriya su fatattake su.

Da yake tabbatar da hakan ga jaridar Leadership, Hakimin Kauyen Mainok, Lawan Tuja Mainok, ya ce ‘yan ta’addan sun mamaye sansanin sojoji da motocin bindigogi shida da misalin karfe 1 na rana kuma suka yi wa sojojin barna.

Hakimin kauyen ya kara da cewa a daidai lokacin da ‘yan ta’addan suka shigo da motocinsu na bindiga, suna harbin iska, wanda hakan ya tilasta mazauna tserewa zuwa gidajensu, yayin da wasu suka gudu zuwa dajin da ke kewaye.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel