Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna

Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna

- An sake kai hari wani yankin jihar Kaduna, in da aka far wa wani Coci tare da sace wasu mutane

- An kuma ruwaito cewa, an hallaka wani likitan ma'aikatar lafiya ta jihar Kaduna yayin harin

- Mazauna yankin sun koka kan harin, inda suke barazanar barin kauyukansu don neman tsira

Har ila yau, ‘yan bindiga sun far wa masu bautar addinin kirista a cocin da ke kauyen Manini Tasha a karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna, a safiyar Lahadi.

An kashe mutum guda, wanda aka bayyana a matsayin likita, yayin da maharan suka sace wasu masu bautar da dama.

Wani ganau, wanda da kyar ya tsere daga abin da ya faru a Cocin na Haske Baptist da ke kauyen Manini, Mista Yakubu Bala, ya shaida wa Leadership cewa ’yan bindigan da ke dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin cocin inda suka yi wa masu ibadan dirar mikiya da misalin karfe 9 na safe.

KU KARANTA: EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna
Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa 'yan bindigan sun zo ne da yawansu, dauke da muggan makamai kuma suka fara yin harbi ba kakkautawa kan masu bautar, wadanda suka yi ta neman tsira a wurare daban-daban.

A cewarsa, “An harbe Dr. Zakariah Dogo Yaro, wani Likita a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna har lahira kuma ba a san adadin mutanen da aka sace ba yayin da dimbin masu ibada suka samu raunuka daban-daban.

“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, ba mu ga wasu mutanen garinmu da suka gudu cikin daji yayin da harbe-harben ke gudana ba.

"Ba mu san abin da ke faruwa ba da yasa muke fuskantar irin wannan yanayin a cikin al'ummominmu masu zaman lafiya ba.

"Yawancin mazauna kauyuka suna barazanar barin gidajensu saboda yawan hare-hare da ake kaiwa kauyuka da yawa a karamar hukumar Chukun,” Yakubu ya koka.

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi Allah wadai da harin, tare da ba da karin haske kan lamarin.

"Hari da sace mutane a cocin Haske Baptist da ke Chikun LG, jihar Kaduna a safiyar abin takaici ne kuma abin Allah wadai ne, na kira kuma na tabbatar da cewa an kashe mutum biyu kuma an yi awon gaba da Shida."

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Ana Ci Gaba da Artabu Tsakanin Sojoji da Boko Haram a Geidam

A wani labarin daban, Wasu ‘yan bindiga sun sace daliban da ba a san adadin su ba daga Jami’ar Green Field da ke jihar Kaduna.

Jaridar TheCable ta fahimci cewa 'yan bindigan sun farma makarantar ne da tsakar daren Talata. An ce sun bude wuta ne don tsoratar da mazauna yankin kafin su sace wasu daliban.

Jami’ar mai zaman kanta tana kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuka a karamar hukumar Chikun, daya daga cikin wuraren da ‘yan bindiga suke a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel