Da duminsa: JAMB ta daga ranar yin jarabawar gwaji ta wannan shekarar

Da duminsa: JAMB ta daga ranar yin jarabawar gwaji ta wannan shekarar

- Hukumar JAMB ta dage ranar rubuta jarabawar gwaji ga daliban da suka yi rijista a wannan shekarar

- Wannan sanarwan na kunshe ne a wata takarda da jami'in hulda da jama'a na hukumar ya fitar a ranar Lahadi

- An mayar da jarabawar zuwa ranar Alhamis, 20 ga watan Mayun 2021 a maimakon 20 ga watan Afirilu

Hukumar JAMB ta daga jarabawar gwajinta da ta saka za a yi a ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu zuwa ranar Alhamis, 20 ga watan Mayun 2021, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda da Fabian Benjamin, shugaban fannin hulda da jama'a na hukumar, yace sauyin ranakun ya biyo baya ne sakamakon wasu 'yan gyare-gyare da hukumar ke yi.

"Sauyin ba zai shafi ranar asalin jarabawar ba da aka saka daga 5 zuwa 19 ga watan Yunin 2021. Ana bukatar daliban da suka yi rijista tare da bukatar zaunawa jarabawar gwajin da su kiyaye sauyin ranakun da aka samu," yace.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun sheke Ikonso, kwamandan IPOB, mashiryin hare-hare a kudu

Da duminsa: JAMB ta daga ranar yin jarabawar gwaji ta wannan shekarar
Da duminsa: JAMB ta daga ranar yin jarabawar gwaji ta wannan shekarar. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kama miyagun ƙwayoyi cikin mutum-mutumin Maryama mahaifiyar Yesu

Yace ya zama dole a sanar da dukkan masu ruwa da tsaki cewa ana cigaba da rijistar UTME kuma za a rufe a ranar 15 ga watan Mayun 2021.

"Hukumar ta gano cewa, wasu masu son rubuta jarabawar na kokarin fara cike muhimman abubuwansu amma suna tura abinda bai dace ba ga 55019 ta layin wayarsu.

"Ana tura NIN ne tare da barin tazara a tsakanin sannan a rubuta lambar NIN din ga 55019. Misali NIN 00000000000."

Yace duk wata hanyar da bata dace ba da aka bi ba zata sa a fara yi wa dalibi rijista ba.

"Ya zama dole mai rubuta jarabawa su gane cewa sai layin wayan da aka hada da NIN ce za a iya amfani da ita wurin rijista," yace.

A wani labari na daban, mayakan ta'addanci na Boko haram a ranar Juma'a sun kai farmaki garinsu mukaddashin shugaban 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a Geidam, jihar Yobe.

Harin Yobe ba shine na farko da kungiyar 'yan ta'addan ke kai farmaki garuruwan shugabannin tsaro ba. Sun taba kai samame kauyukan tsohon shugaban sojin sama, marigayi Alex Badeh da tsohon shugaban sojin kasa, Tukur Buratai, a jihohin Adamawa da Borno yayin da suke aiki.

Maharan sun kutsa garin a ranar Juma'a da yammaci kafin daga bisani jiragen yaki su bayyana tare da sakar musu ruwan wuta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel