An kama miyagun ƙwayoyi cikin mutum-mutumin Maryama mahaifiyar Yesu
- Masu safarar miyagun kwayoyi sun shiga hannun jami'an NDLEA bayan kama su da aka yi da tarin kwayoyi
- Salonsu shine na dankara miyagun kwayoyin a mutum-mutumin Maryama, mahaifiyar annabi Isah
- An kama wasu miyagun kwayoyin a cikin safayar bangarorin ababen hawa inda za a tura su Dubai da Canada
Masu safarar miyagun kwayoyi dake neman hanyar boye miyagun ayyukan su sun yanke hukuncin ci da addini ta hanyar dankara miyagun kwayoyin a gunkin Maryama, mahaifiyar annabi Isah.
Hukumar yaki da safara tare da hana fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama kamfanoni biyu da suka boye miyagun kwayoyi a a gunkin da kuma wasu safayar bangarorin ababen hawa da za a kai kasashen Canada da daular Larabawa.
An samu sinkin kwayoyin methamphetamine mai nauyin gram 140 da aka zuba a gunkin Maryama wanda za a kaiwa wasu 'yan kasar Philippine, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji
An samu wasu sunkin masu nauyin gram 500 da aka boye a safayar bangarorin ababen hawa da za a kai kasar Canada.
Wani pakiti mai girman kilogram 3.1 an same shi na wiwi a cikin wasu kayan dandano da kuma wani sinkin kilogram daya da aka samu a cikin magungunan gargajiya da za a kai Dubai, kamar yadda Femi Babafemi, daraktan yada labarai na NDLEA ya tabbatar.
A wani cigaba makamancin hakan, NDLEA ta cafke wasu mutum 31 daga jihar Ondo da aka kama da kilogram 276 na miyagun kwayoyi, daga cikinsu akwai mata bakwai.
An kama su ne a samamen makonni biyu da aka yi wanda aka fara a ranar 6 ga watan Afirilu.
Babafemi yace an fara samamen domin shawo kan yadda amfani da miyagun kwayoyi ya yawaita tsakanin matasa da tsoffi a jihar Ondo.
KU KARANTA: Hoton motocin alfarman miloniya Ahmed Musa masu darajar N200m sun gigita jama'a
A wwani labari na daban, jami'an hukumar yaki da miyagun kwayoyi da fasa-kwabrinsu (NDLEA) ta kama wani matashi mai suna Chibuike Apolos, a kan zarginsa da zama gawurtaccen mai siyar da miyagun kwayoyin da ta dade tana nema a jihar Abia.
Femi Babafemi, kakakin hukumar, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.
Babafemi yace an kama Apolos a ranar Laraba yayin wani samamen sassafe da jami'an suka kai maboyarsa dake yankin Isialangwa dake jihar. Sun same shi da sama da 100kg na miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng