Boko haram sun kai hari garin sabon IGP, sun rabawa jama'a wasiku

Boko haram sun kai hari garin sabon IGP, sun rabawa jama'a wasiku

- A yammacin Juma'a ne mayakan ta'addanci na Boko haram suka kutsa garinsu sabon IGP, Usman Alkali Baba

- Sun shiga har tsakiyar garin Geidam dake jihar Yobe inda suka dinga harbe-harbe tare da kona shagunan jama'a

- Tuni jiragen yakin sojoji tare da taimakon dakarun sojin kasa, suka fatattaki 'yan ta'addan inda suka tsere

Mayakan ta'addanci na Boko haram a ranar Juma'a sun kai farmaki garinsu mukaddashin shugaban 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a Geidam, jihar Yobe.

Harin Yobe ba shine na farko da kungiyar 'yan ta'addan ke kai farmaki garuruwan shugabannin tsaro ba.

Sun taba kai samame kauyukan tsohon shugaban sojin sama, marigayi Alex Badeh da tsohon shugaban sojin kasa, Tukur Buratai, a jihohin Adamawa da Borno yayin da suke aiki.

Maharan sun kutsa garin a ranar Juma'a da yammaci kafin daga bisani jiragen yaki su bayyana tare da sakar musu ruwan wuta.

KU KARANTA: Labarin Sheke Mahamat Deby da ya karba mulkin Chadi: Menene gaskiyar lamarin?

Boko haram sun kai hari garin sabon IGP, sun rabawa jama'a wasiku
Boko haram sun kai hari garin sabon IGP, sun rabawa jama'a wasiku. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KUKARANTA: Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki

Wata majiya ta sanar da Punch cewa maharan sai da suka isa tsakiyar garin sannan suka fara harbe-harbe tare da kona shaguna, hakan yasa dakarun soji suka hau ta kansu.

Dole ta sa mazauna garin suka rufe kansu a gidajensu amma wasu suka gangara dajikan dake da kusanci da nan suka boye.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Abdulkarim Dungus, ya tabbatar da aukuwar harin.

A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da miyagun kwayoyi da fasa-kwabrinsu (NDLEA) ta kama wani matashi mai suna Chibuike Apolos, a kan zarginsa da zama gawurtaccen mai siyar da miyagun kwayoyin da ta dade tana nema a jihar Abia.

Femi Babafemi, kakakin hukumar, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Babafemi yace an kama Apolos a ranar Laraba yayin wani samamen sassafe da jami'an suka kai maboyarsa dake yankin Isialangwa dake jihar. Sun same shi da sama da 100kg na miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa, wanda ake zargin babban mai rarraba miyagun kwayoyi ne ga masu siyarwa kuma tun a watan Fabrairu hukumar ke nemansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel