Jami'an tsaro sun sheke Ikonso, kwamandan IPOB, mashiryin hare-hare a kudu
- Tawagar jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda, jami'an DSS da na rundunar soji sun kai samame sansanin IPOB a Imo
- Sun yi nasarar sheke kwamandan IPOB Ikonso kuma shugaban kungiyar a kudu kuma mashiryin miyagun hare-hare
- Sun hada da wasu mutum 6 bayan musayar wuta da suka yi kuma an samu miyagun makamai da harsasai
Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da takwarorinsu na rundunar soji da farin kaya, a wani aikin hadin guiwa da suka yi a sa'o'in farko na ranar Asabar, sun tsinkayi hedkwatar 'yan ta'addan IPOB dake kauyen Awomama dake karamar hukumar Oru ta gabas a jihar Imo inda suka halaka 'yan tada kayar baya.
'Yan ta'addan ne suke da alhakin kai hari hedkwatar 'yan sandan jihar da gidan gyaran hali a ranar 5 ga watan Afirilun 2021.
Sun kai wasu jerin farmaki ga jami'an tsaro da wurare da suke a yankunan kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan.
KU KARANTA: Hotunan amfanin gona da Dan Najeriya ke shukawa a iska sun bada matukar mamaki
KU KARANTA: Bidiyo: Magidanci ya bada labarin yadda ya dirkawa sirikarsa ciki, ta haifo namiji
Rahotannin sirri da PRNigeria ta samu ta tabbatar da cewa jami'an tsaro sun tunkari sansanin 'yan ta'addan inda tsagerun suka dinga sakar musu ruwan wuta.
"Cike da kwarewa da zakakuranci, rundunar tsaron hadin guiwan suka yi martani. Daga bisani sun halaka gagararren kwamandan IPOB na kudu maso gabas da aka fi sani da Ikonso tare da wasu mayaka masu makamai.
"An san kwamanda Ikonso a matsayin mataimakin shugaban kungiyar kuma mai shugabantar ayyukan tsageranci na kungiyar. Shine mashiryin harin hedkwatar 'yan sandan Imo da kuma sauran wuraren jami'an tsaro.
"Aikin na daga cikin kokarin 'yan sandan da sauran jami'an tsaro wurin shawo kan ta'addanci a jihohin kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan," majiyar tace.
Bayan artabun ruwan wuta, jami'an tsaro sun samu gawar Ikonso kwamanda da wasu mayaka 6. An samu miyagun makamai masu tarin yawa da suka hada da AK47, daruruwan harsasai, layu da sauransu.
A yayin rubuta wannan rahoton, 'yan sanda uku da soja daya suna karbar taimakon masana lafiya sakamakon miyagun raunikan da suka samu yayin musayar wutar.
A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da miyagun kwayoyi da fasa-kwabrinsu (NDLEA) ta kama wani matashi mai suna Chibuike Apolos, a kan zarginsa da zama gawurtaccen mai siyar da miyagun kwayoyin da ta dade tana nema a jihar Abia.
Femi Babafemi, kakakin hukumar, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.
Babafemi yace an kama Apolos a ranar Laraba yayin wani samamen sassafe da jami'an suka kai maboyarsa dake yankin Isialangwa dake jihar. Sun same shi da sama da 100kg na miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng