Da dumi-dumi: Ana Ci Gaba da Artabu Tsakanin Sojoji da Boko Haram a Geidam

Da dumi-dumi: Ana Ci Gaba da Artabu Tsakanin Sojoji da Boko Haram a Geidam

- 'Yan ta'addan Boko Haram sun ci gaba da aika-aikata a garin Geidam dake jihar Yobe a arewaci

- An ruwaito cewa, har yau da safiyar Lahadi ana ci gaba da luguden wuta tsakanin 'yan ta'adda da sojoji

- Dan majalisa mai wakiltar yankin a tarayya ya shaida yadda a'ummarsa ke cikin mawuyacin hali

Ana ci gaba da luguden wuta tsakanin sojojin Najeriya da masu tayar da kayar baya na kungiyar ISWAP a Geidam, jihar Yobe, Arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan ta'addan sun dawo garin Geidam ne 'yan sa'o'i bayan da suka janye bayan da aka shafe sama da awanni 24 suna yi wa garin kawanya, farawa daga ranar Juma'a, 23 ga Afrilu.

An samu labarin a safiyar Lahadi cewa sojojin Najeriya da masu tayar da kayar baya a halin yanzu suna artabu sosai sakamakon wani sabon hari.

KU KARANTA: Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati

Da dumi-dumi: Ana Ci Gaba da Artabu Tsakanin Sojoji da Boko Haram a Geidam
Da dumi-dumi: Ana Ci Gaba da Artabu Tsakanin Sojoji da Boko Haram a Geidam Hoto: cnn.com
Asali: UGC

Wasu Mazauna Geidam tuni suka tsere sakamakon rikicin. Akwai fargabar cewa adadin masu tayar da kayar baya a cikin rundunar ya karu.

Ko da yake Sojojin Najeriya a ranar Asabar, 24 ga Afrilu sun ce, sun yi mummunan rauni a kan mayakan ISWAP a yayin artabun na baya, wani dan majalisar tarayya da ke musanta ikirarin.

Premium Times ta ruwaito cewa Lawan Shettima, dan majalisa mai wakiltar mazabar Geidam, Yunusari da Bursari a Majalisar Tarayya, ya ce har yanzu maharan suna da iko da garin Geidam.

“Zan iya gaya muku cewa wadannan maharan sun mamaye Geidam. Kuna iya ganin bidiyo da hotuna yayin da suke motsawa suke ta kona abin da suka ga dama,” in ji Shettima.

Dan majalisar ya kuma ce 'yan mazabarsa “sun kasance a karkashin rahamar kungiyar Boko Haram sama da awanni 24 ba tare da wani kalubale ba."

KU KARANTA: EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

A wani labarin, Rundunar sojojin Nigeria ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole, a ranar Juma'a, ta ce dakarunta sun kashe ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram/ISWAP a garin Geidam a Yobe.

Hakan na zuwa ne bayan rahotonni da ke nuna cewa ƴan ta'addan sun sake kai hari Geidam a ranar Juma'a kmar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar sojojin, Mohammed Yerima, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya ce sojojin sun kwato motocci masu bindiga da wasu makaman yayin artabu da yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel