Dakarun Sojoji Sun Aika Ƴan Boko Haram 21 Lahira a Geidam

Dakarun Sojoji Sun Aika Ƴan Boko Haram 21 Lahira a Geidam

- Rundunar Sojojin Nigeria ta ce sojoji sun halaka ƴan ta'addan Boko Haram 21 a garin Geidam

- Mohammed Yerima, kakakin soji ya ce sojojin sun ƙwato motocci masu bindiga da makamai

- Yerima ya kuma ce sojoji uku sun jikkata yayin harin amma suna murmurewa a asibiti

Rundunar sojojin Nigeria ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole, a ranar Juma'a, ta ce dakarunta sun kashe ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram/ISWAP a garin Geidam a Yobe.

Hakan na zuwa ne bayan rahotonni da ke nuna cewa ƴan ta'addan sun sake kai hari Geidam a ranar Juma'a kmar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dakarun Sojoji Sun Aika Ƴan Boko Haram 21 Lahira a Geidam
Dakarun Sojoji Sun Aika Ƴan Boko Haram 21 Lahira a Geidam. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ba Makiyaya Fulani Ke Kisa Ba, Baƙi Ne Suka Shigo Nigeria, Gwamna Ikpeazu

Kakakin rundunar sojojin, Mohammed Yerima, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya ce sojojin sun kwato motocci masu bindiga da wasu makaman yayin artabu da yan ta'addan.

Ya ce sojojin da ke aikin Operation Tura Takaibango sun yi fafata da ƴan ta'addan a lokacin da suka kai hari a garin a ranar Juma'a, inda suka lalata kayayyakin sadarwa tare da satar kayan masarufi.

A cewarsa, sojojin da suke garin tare da taimakon sojojin sama sun fatattaki ƴan bindigan inda suka kashe 21 cikinsu.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Yerima ya ce har yanzu sojojin na sintiri a garin ko za su gano wasu ƴan ta'addan domin wasu da dama sun tsere da raunin bindiga.

Ya ce sojoji uku sun jikkata sakamakon artabu amma sun fara samun sauki a asibitin sojoji.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel