EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

- Hukumar EFCC ta kame wasu da take zargin masu aikata laifuka ne ta kafar yanar gizo

- Hukumar ta kame wani dan kasuwa mai ta'ammuli da haramtattun kudin intanet, Bitcoin

- Hukumar ta shaida cewa, za ta gurfanar dasu a kotu idan ta kammala binciken da ya dace

Ofishin shiyyar Ibadan na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Zagon Kasa (EFCC) ya kama wani dan kasuwar bitcoin da laifin aikata zamba a yanar gizo, Premium Times ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Ayomide Adebowale, an kama shi a ranar Juma’a, tare da wasu mutum hudu daga wasu wurare biyu a yankin Elebu da ke Ibadan ta Jihar Oyo.

EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata
EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana sauran da aka kama da suna Philip Gabriel, Mayowa Jolaoso Segun, Babatunde Segun Adeyinka da Abiodun Tolulope Emmanuel.

KU KARANTA: Muna son ganin Buhari: Mata 'yan kasuwa sun koka kan tsadar abinci

EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata
EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya fada cikin wata sanarwa cewa shekarunsu sun kai tsakanin 21 zuwa 37.

“An kama su ne a bayan samun bayanan sirri da Hukumar ta samu kan zarginsu da aikata laifuka masu nasaba da yanar gizo.

EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata
EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Abubuwan da aka kwato daga wurinsu sun hada da motoci biyu, kwamfyutocin tafi-da-gidanka, wayoyi da wasu takardu da ake zargin suna dauke da bayanan bogi.

EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata
EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

"Za a gurfanar da su zuwa kotu da zarar an kammala bincike," in ji shi.

KU KARANTA: Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista

A wani labarin daban, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ya ce an yi kutse a shafinsa na Facebook amma yanzu an dawo da shi.

A ranar Litinin, Mista Pantami ya ruwaito cewa an yi kutse a shafinsa na sada zumunta. “An yi kutse a wannan asusun. Yanzu aka dawo dashi. Ba Dr Isa Ali Pantami bane ke kula dashi, wasu matasa ne suke kulawa dashi.

Ku yi watsi da duk wata bukata, tsokaci ko sako daga gare ta,” ya rubuta ta wannan shafin a daren Litinin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel