Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi

- Sheikh Ahmad Mahmoud Gumi ya kwana biyu bai shiga daji ganawa da yan bindiga ba

- Wannan ya biyo bayan caccakan da wasu mutane suke masa

- Sheikh Gumi ya ce kawai ya daina ne saboda matsayar da gwamnatin jihar ta dauki

Shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ya daina sulhu da yan bindiga ne saboda gwamnatin jihar ta nuna ba ta son haka.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai jami'ar Greenfield dake hanyar Abuja-Kaduna inda sukayi awon gaba da dalibai kuma suka kashe mutum daya.

Yan bindigan sun bukaci N800m a matsayin kudin fansa.

Yayin magana da SaharaReporters ranar Alhamis, hadimin Gumi, Salisu Hassan, ya ce Malamin ya daina tafiya sulhu da yan bindigan ne don bin umurnin gwamnatin jihar.

"A'a, Sheikh ba wai yana da wasu ayyuka bane. Matsalar itace gwamnati ta ce bata son a yi sulhu da wadannan mutane," Hassan yace.

"Saboda haka Sheikh yana kokarin samar da wasu hanyoyin cimma manufarsa. Gwamnatin jihar ta ce ba ta son sulhu."

KU DUBA: Majalisar dattawa ta amince Buhari ya sake cin bashin sama da Tiriliyan 1

Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi
Dalilin da ya sa na daina sulhu da yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi Credit: Ahmad Gumi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

Za ku tuna cewa Gumi ya shiga dazuka daban-daban a Arewa maso yammacin Najeriya don yiwa yan bindiga wa'azin suun ajiye makamansu, su yi sulhu da gwamnati, amma El-Rufa'i ya nuna baya son hakan.

Gwamnan jihar ya ce zai hukunta duk wanda yayi sulhu da yan bindiga da sunan gwamnati.

A bangare guda, an tabbatar da sace wasu ma'aikatan jinya guda biyu a babban asibitin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna da safiyar ranar Alhamis.

Daraktan asibitin, Dakta Shingyu Shamnom, wanda ya tabbatar wa da jaridar Leadership faruwar lamarin, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun afkawa babban asibitin ne ta hanyar haura katanga dauke da muggan makamai.

A cewarsa, yayin da 'yan fashin ke harbi ba kakkautawa a harabar asibitin, wasu malaman jinya biyu da ke aikin dare sun fito sun bayyana kansu a matsayin ma'aikatan lafiya kuma' yan fashin sun tafi da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel