Da duminsa: Majalisar dattawa ta amince Buhari ya sake cin bashin sama da Tiriliyan 1

Majalisar dattawa a ranar Laraba ta amincewa gwamnatin tarayya ta karbi sabon bashin $1.5bn da €995m daga kasashen waje.

A lissafin da muka buga, wannan kudi ya kama N1.1tr a kudin Najeriya.

Sanatocin sun amince gwamnati ta karbi wannan bashi ne bayan kwamitin basussuka na majalisa ta gabatar da rahotonta kan shirin karban bashin gwamnatin tarayya.

Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia, ya gabatar da rahoton.

Da duminsa: Majalisar dattawa ta amince Buhari ya sake cin bashin sama da Tiriliyan 1
Da duminsa: Majalisar dattawa ta amince Buhari ya sake cin bashin sama da Tiriliyan 1
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel