Karin bayani: An kashe mutum daya, an sace dalibai a jami'ar GreenField a Kaduna

Karin bayani: An kashe mutum daya, an sace dalibai a jami'ar GreenField a Kaduna

- Yan bindiga sun kai mumunan hari jami'ar Greenfield da dare

- An kashe jami'in ma'aikacin guda daya yayin awon gaba da su

- Ba'a san adadin daliban da aka sace ba har yanzu

Hukumar yan sanda jihar Kaduna, ta tabbatar da labarin harin da yan bindiga suka kai jami'ar Greenfield dake hanyar Abuja-Kaduna inda sukayi awon gaba da dalibai.

Rahoto ya nuna cewa yan bindigan sun dira makarantar ne misalin karfe 8:35 na dare.

Kakakin hukumar yan sanda, Mohammed Jalige, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai ranar Laraba cewa an yi awon gaba da wasu dalibai.

Jalige ya kara da cewa ba'a san adadin daliban da aka sace ba har yanzu.

Ya ce an tura jami'an tsaro wajen domin bibiyan yan bindigan tare da ceto daliban.

Jami'ar Greenfield na kan titin Abuja-Kaduna, kusa da masana'antar Olam.

DUBA NAN: Majalisar dattawa ta amince Buhari ya sake cin bashin sama da Tiriliyan 1

Yanzu-yanzu: Hukumar ta tabbatar da an sace dimbin dalibai a jami'ar GreenField a Kaduna
Yanzu-yanzu: Hukumar ta tabbatar da an sace dimbin dalibai a jami'ar GreenField a Kaduna
Asali: UGC

KU KARANTA: An garƙame hedkwatar kamfanin lantarki na Kaduna saboda ƙin biyan harajin N464m

Hakazalika kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa bayan sintiri da bibiyan sahun yan bindigan, an tabbatar da kisan daya daga cikin ma'aikatan jami'ar.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba a Facebook.

"Bayan bincike da sintiri, an tabbatar da kisan Paul Ude Okafor, wani ma'aikacin jami'ar, yayinda akayi awon gaba da dalibai," yace.

"Jami'an tsaro sun dauke sauran daliban kuma sun dankasu ga hukumar makarantar misalin karfe 12 na ranar Laraba, 21 ga Afrilu, 2021."

"Har yanzu ana neman sanin adadin daliban da aka sace."

A bangare guda, Iyayen dalibai 39 da aka sace a kwalejin FCFM Afaka Kaduna sun ce sun biya milyan 17 don sakin dalibansu amma yan bindigan mutum 10 kawai suka saki cikinsu.

A binciken da Jaridar Leadership tayi ikirarin gudanarwar, iyayen daliban sun biya kudin ne don a sake musu yaransu gaba daya amma goma kadai yan bindigan suka saki.

Wani mahaifi wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace, "yan bindigan sun yarda zasu saki yaranmu idan muka biyasu kudin, sai muka tara muka biyasu amma mutum goma kadai suka saki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel