Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da ma’aikatan jinya 2 da ke bakin aiki a Kaduna

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da ma’aikatan jinya 2 da ke bakin aiki a Kaduna

- Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan jinya guda biyu a babban asibitin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna

- Lamarin ya afku ne da sanyin asubahin Alhamis, 22 ga watan Afrilu

- Maharan sun kai farmaki asibitin ne ta hanyar haura katanga sannan suka dunga harbi ba kakkautawa

An tabbatar da sace wasu ma'aikatan jinya guda biyu a babban asibitin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna da safiyar ranar Alhamis.

Daraktan asibitin, Dakta Shingyu Shamnom, wanda ya tabbatar wa da jaridar Leadership faruwar lamarin, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun afkawa babban asibitin ne ta hanyar haura katanga dauke da muggan makamai.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC Kaduna ta kafa tarihi a Najeriya, ta gudanar da jarrabawa ga masu neman kujerun ciyamomi

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da ma’aikatan jinya 2 da ke bakin aiki a Kaduna
Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da ma’aikatan jinya 2 da ke bakin aiki a Kaduna Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

A cewarsa, yayin da 'yan fashin ke harbi ba kakkautawa a harabar asibitin, wasu malaman jinya biyu da ke aikin dare sun fito sun bayyana kansu a matsayin ma'aikatan lafiya kuma' yan fashin sun tafi da su.

"Lokacin da muka ji karar harbe-harbe, mun kasance a gidajen mu mabanbanta, har sai da aka kira mu cewa masu satar mutane ne suka mamaye asibitin, sai kawai muka gano cewa yan fashin sun da tafi malaman jinya biyu da ke aikin dare," in ji shi.

Dr. Shingyu ya kara da cewa "masu garkuwar sun tafi da wayar wani ma'aikacin wanda muke tsammanin shima an sace shi amma daga baya ya dawo."

Shugaban karamar hukumar Kajuru, Hon. Cafra Casino, lokacin da aka tuntube shi ya tabbatar da sace ma'aikatan jinyar biyu daga Babban Asibitin Kajuru.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin don haka ya bukaci mutanen yankin da su kwantar da hankulansu.

KU KARANTA KUMA: An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6

A gefe guda, sufetan yan sanda na riƙo (IGP), Usman Alƙali Baba, ya ƙara yin kira da a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin bata damar sauke nauyin dake kanta na daƙile ƙaruwar rashin tsaro a cikin ƙasa.

Yayi wannan kira ne a lokacin da ya ziyarci kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ranar Laraba kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

IGP ɗin yace ya kawo wannan ziyara ne domin yin godiya ga Gbajabiamila da sauran yan majalisu bisa goyon bayan da hukumar yan sanda ke samu daga yan majalisun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel