Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

Jiya Laraba, 21 ga watan Afrilu, 2021, jihohin Najeriya akalla biyar sun fuskanci hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane.

Jihohin da aka kaiwa wadannan hare-hare sun hada da jihar Enugu, Kaduna, Oyo, Ondo, Zamfara da Neja.

1. An kashe yan sanda biyu a jihar Enugu

A ranar Laraba, wasu yan bindiga sun kai hari hedkwatar hukumar yan sandan dake Adani, karamar hukumar Uzo-Uwani na jihar Enugu.

Kwamandan yan sandan yankin Nsukka, Hassan Yahaya, ya tabbatar da harin.

Wata majiya ta bayyanawa kamfanin dillancin Najeriya NAN cewa an kashe yan sanda biyu kuma an bankawa ofishin yan sandan wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

2. An kashe ma'aikaci guda, an kwashe dimbin dalibai a jami'ar GreenField dake Kaduna

Hukumar yan sandan jihar Kaduna, ta tabbatar da labarin harin da yan bindiga suka kai jami'ar Greenfield dake hanyar Abuja-Kaduna inda sukayi awon gaba da dalibai.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa bayan sintiri da bibiyan sahun yan bindigan, an tabbatar da kisan daya daga cikin ma'aikatan jami'ar.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba a Facebook.

"Bayan bincike da sintiri, an tabbatar da kisan Paul Ude Okafor, wani ma'aikacin jami'ar, yayinda akayi awon gaba da dalibai," yace.

"Jami'an tsaro sun dauke sauran daliban kuma sun dankasu ga hukumar makarantar misalin karfe 12 na ranar Laraba, 21 ga Afrilu, 2021."

"Har yanzu ana neman sanin adadin daliban da aka sace."

Yan bindigan sun bukaci N800m a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnati Ta Tanadi N470bn Don Karawa Malaman Jami'a Albashi Da Gyara Jami'a

A cewar rahoton TheNation, yan bindigan sun yi barazanar kashe daliban idan ba'a biya kudin ba.

Munanan hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane 5 da ya suka auku jiya Laraba
Munanan hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane 5 da ya suka auku jiya Laraba Credit: @PoliceNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wadanda suka daliban Kaduna sun bukaci N800m matsayin kudin fansa

3. An hallaka jami'in Amotekun a jihar Oyo

An hallaka jami'in Amotekun, Suleiman Quadri, a jihar Oyo.

Rahoton TheNation ya nuna cewa wasu yan bindiga sun hallaka Quadri ne yayinda yake raka wasu manoma gona a Fiditi.

Yan bindigan sun bude masa wuta tare da abokin aikinsa, Amoo Yisau, wanda ya tsallake rijiya da baya.

Yisau na jinya yanzu a asibiti kuma tuni an bizne Quadri bisa koyarwar addinin Musulunci.

Kwamandan Amotekun, Col. Olayinka Olayanju (rtd), ya tabbatar da labarin.

4. An yi awon gaba da ma'aikata 3 a Ondo

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ma'aikatan gine-gine a hanyar Ikaram-Akunnu-Akoko a jihar Ondo.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai harin ne da tsakar rana.

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Har yanzu ba'a tuntubi iyalansu ba.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da harin kuma yace an tura jami'an tsaro bibiyansu.

KU KARANTA: Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

5. Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun bankawa barikin Soji wuta a Neja

Wasu ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai 60 a safiyar ranar Laraba sun mamaye wani sansanin sojoji da ke garin Zazzaga, Munya, Jihar Neja.

A yayin harin, mayakan sun yi artabu da sojoji, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama.

Harin na baya-bayan nan da aka kai kan wani sansanin sojoji a jihar ya zo ne kusan makonni uku bayan da wasu gungun ‘yan fashi suka kai hari kan rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da ke Allawa da Basa a Shiroro, inda suka kashe sojoji biyar da wani dan sanda.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekara 20 Da Ake Zargin Yana Garkuwa Da Mutane, Sun Kwato Kayayyaki

Ba kamar mamayewar Allawa da Basa ba, babu wani soja da aka kashe a wannan sabon harin; sai dai, an tabbatar da batan wani soja a daidai lokacin kawo wannan rahoton, jaridar Sun ta ruwaito.

Yan bindigan sun bankawa motocin Soji da dakin ajiyar kayan abincinsu wuta.

An kafa sansanin Sojin ne a 2017 sakamakon hare-haren yan bindiga a yankin.

6. An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6

Wasu mutane da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun jefa jihar Zamfara cikin jimami da juyayi bayan da suka kaddamar da hare-hare a garuruwa shida a ranar Laraba, 21 ga Afrilu, inda suka kashe akalla mutane 45.

A cewar jaridar Daily Trust, mutane da dama da suka hada da mata da yara sun bata a sanadiyyar hare-haren.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun kuma lalata shaguna da gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng