Shugaba Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa

Shugaba Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa

- Shugaban ƙungiyar yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, ya ce shugaba Buhari ne babban wanda baison ganin cigaban Najeriya

- Adebanjo yace ba yadda za'a yi sojoji su ƙaƙabama yan Najeriya wannan kundin tsarin mulkin tun 1966 amma Buhari yaƙi yarda a canza shi kuma yace shi mai kishin ƙasa ne

- Yace shugaba Buhari da jam'iyyar sa ta APC sune ummul aba'isin duk rikicin da ake samu na rarrabuwar kawunan yan Najeriya

Shugaban ƙungiyar yarbawa, Afenifere, Chief Ayo Adebanjo, yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shine babban maƙiyin haɗin kan Najeriya.

Adebanjo ya faɗi hakane a shirin safe na gidan talabashin ɗin Arise News mai suna 'Morning show'.

KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani

Yace shugaban shine ya buɗe ƙofa ga duk wani rabe-rabe da ake samu a ƙasar nan saboda watsin da yayi da kiran da masu kaunar Najeriya ke masa na yin sabon kundin tsarin mulki.

Ya kuma kara da cewa sojoji ne suka ƙaƙaba wa yan Najeriya kundin tsarin mulki 1999 (wanda aka gyara), kuma ya zama wajibi a canza shi.

Kuma Ya zargi kundin tsarin mulkin da yin rashin adalci ga wasu yankunan ƙasar nan.

Ya ce sabon kundin ne kaɗai zai iya rufe bakin masu tsegumi irin su Nnamdi Kanu da Sunday Igboho kafin zuwan zaɓen 2023 kamar yadda PM News ta ruwaito.

Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa
Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Adebanjo yace:

"Tun da shugaba Buhari yaki sauraran masu kira da a canza kundin tsarin mulki, hakan ya jawo masu tsegumi suka cigaba da aikinsu daga sassa daban-daban na ƙasar nan. Kuma hakan ne ya ƙara kawo rarrabuwar kai tsakanin yan Najeriya."

"Wannan ya nuna ƙarara cewa Buhari shine babban makiyin haɗin kan Najeriya tunda yaki amincewa da buƙatar al'ummar da yake mulka."

Adebanjo ya zargi Buhari da boyayyar manufa saboda ƙin amincewarsa wajen sake fasalta Najeriya.

KARANTA ANAN: Bincike: Mafi yawancin Gwamnonin dake kan madafun iko sun fito ne daga wannan jami'ar

Yace matasan yanzun basu da hakuri kuma bazasu iya ɗaukar wannan wahalhalun ba waɗanda wannan kundin tsarin mulkin na yanzun yake jawo musu.

Yace: "An ƙaƙaba ma yan Najeriya wannan kundin tsarin mulkinne a shekarar 1966, Kuma shine babban dalilin rikicin dake faruwa yanzun."

"Dole mu canza fasalin ƙasar nan, mu maidata asalin tsarin mulkin jamhuriya kamar yadda iyayen mu suka yi kokarin gina ta."

Daga ƙarshe yace ƙin amincewar shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC wajen sake sabon kundin tsarin mulki, ya bayyana cewa dashi da jam'iyyar sa sune manyan maƙiyan haɗin kan ƙasar nan.

A wani labarin kuma Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama

Wani jami'in ɗan sanda da yasha lambar yabo daga wajen gwamnan jihar Lagos, ASP Sunday Erhabor, ya bayyana wasu ƙalubale da ya fuskanta lokacin da yake kan aiki.

Daga cikin ƙalubalen da ya faɗa, jami'in yace akwai wata mata da ta taɓa marinsa a gaban mijinta lokacin yana kan aikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel