Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani

Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani

- Tsohon daraktan hukumar tsaro ta DSS, Dennis Amachree, yace sai da suka binciko komai game da Ministan sadarwa, Isa Pantami, kafin naɗinsa a matsayin minista

- Amachree ya bayyana babban dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken hukumar har aka naɗa shi ministan sadarwa

- A cewarsa bayan sun gama aikin su, sun mika ma gwamnatin tarayya da yan majalisu rahoton da suka gano, amma duk da haka suka amince da shi

Tsohon daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Dennis Amachree, yace hukumar DSS ta gudanar da bincike a kan ministan sadarwa, Dr. Isa Pantami, kafin a tabbatar dashi a matsayin minista a shekarar 2019.

Amachree yayi wannan jawabi ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar Punch a shirin 'The Roundtable'.

KARANTA ANAN: Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed

Yace wajibine duk wani minista ya tsallake binciken DSS da kuma na yan majalisu kafin a tabbatar masa da muƙaminsa.

Pantami, wanda tsohon daraktan hukumar kula da fasahar sadarwa (NITDA), shine kaɗai ɗan majalisar zartarwa da ya fito daga jihar Gombe.

A kwanan nan dai an huro ma Pantami wuta saboda wasu kalamai da ya yi a baya kan wasu ƙungiyoyin ta'addanci da suka haɗa da Taliban da Alƙa'ida.

Sai dai ministan ya fito fili ya bayyana cewa ya canza waɗannan kalaman, inda yace a yanzun ya ƙara ilimi da gogewa.

Amma duk da haka wasu yan Najeriya sun cigaba da kiran ya sauka daga muƙaminsa.

A jawabin da yayi lokacin tattaunawar, tsohon daraktan DSS ɗin yace yakamata Ministan ya ajiye muƙaminsa domin yana da wahala mutune irinsa su canza.

Ya ce hukumar DSS ɗin tana da dukkan bayanan ɗai-ɗaikun mutane, ya ƙara da cewa hukumar tana sane da kalaman da ministan yayi a baya kuma ta miƙa ma gwamnatin tarayya da yan majalisu rahoton bincikenta.

Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani
Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Amachree ya ce:

"Babu wani bayani da yake guje ma DSS, muna da bayanan gaba ɗaya. Lokacin da nike aiki a hukumar, muna aje kundin bayanan kowane mutum wanda tauraruwarsa ke haskawa a ƙasar nan."

"A duk lokacin da aka zaɓi wani za'a bashi muƙamin minista, kwamishina ko wani muƙami, za'a turama DSS sunanshi domin bincike.

"Zasu binciki tushenka har sai takai ga kakar ka mace, zasu binciki karatunka har zuwa makarantar firamare. Sannan kuma zasu duba dukkan al'amuranka na yau da kullum. Kuma ina mai tabbatar muku da cewa wannan lamarin na Pantami mun daɗe da saninshi."

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

Ya kuma ƙara da cewa lamarin Pantami akwai siyasa a cikinsa. Yace idan aka naɗa wani mutum a wani muƙami kuma hukumar tsaro ta gano wani abu a tattare dashi, zasu tura ma hukumomin dake son naɗa shi abinda suka gano.

Amachree yace daga nan komai zai koma hannun su, idan sunga dama su amince da naɗinshi in basu ga dama ba su canza wani.

Tsohon darakatan DSS ɗin ya kuma bayyana cewa Amurka na ƙoƙarin haɗa bayanai a kan ministan sadarwar yanzu.

Yace: "Pantami ya miƙa sunanshi ga sashen tattara bayanai na US (US database), kuma bincike akan mutane ba lokaci ɗaya ake yinsa ba. Wannan yawaitar maganganun mutanen akansa shine ya jawo hankalin ofishin jakadancin Amurka."

"Nasan zasu tsananta bincike a kan asalinsa, zasu saka ido akanshi yanzun. Da zarar lamarin ya baci zasu hana shi zirga-zirga."

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Inji Ministan Tsaro

Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci.

Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel