Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama
- Wani jami'in ɗan sanda mai suna, Sunday Erhabor, ya bayyana wasu manyan ƙalubalen da ya taɓa fuskanta a lokacin yana cikin aiki
- Ɗan sandan yasha lambar yabo daga wajen gwamnan jihar Lagos saboda halin dattako, hakuri da juriya da ya nuna a lokacin da wani mai laifi ya ci mutuncinsa a yankin Oniru na jihar Lagos
- Erhabor yace ɗaya daga cikin abunda yake iya tunawa shine wata mata ta mare shi a gaban mijinta lokacin yana cikin aiki, amma bai nuna mata fushinsa ba
Wani jami'in ɗan sanda da yasha lambar yabo daga wajen gwamnan jihar Lagos, ASP Sunday Erhabor, ya bayyana wasu ƙalubale da ya fuskanta lokacin da yake kan aiki.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu
Daga cikin ƙalubalen da ya faɗa, jami'in yace akwai wata mata da ta taɓa marinsa a gaban mijinta lokacin yana kan aikinsa.
Ɗan sandan mai kimanin shekaru 53 a duniya ya jawo hankalin masu amfani da kafar sada zumunta bisa halin dattako da hakurin da yayi lokacin da wani mai laifi, Victor Ebhomenyen, yaci mutuncinsa a yankin Oniru, jihar Lagos.
A wata tattaunawa da yayi da jaridar Punch, Erhabor, wanda ya shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1992, ya bayyana wani ƙalubalen da ya taɓa fusakanta a aikinsa.
Erhabor yace:
"Bazan iya tuna komai ba amma akwai ƙalubale dayawa. Akwai wani da ya faru lokacin ina Festac, muna kan aikin binciken kwakwaf a hanyar Okota, na tsaida wata mota wadda wata mata da mijinta ke ciki."
KARANTA ANAN: Jami'o'i keda ƙarfin ikon ɗaukar sabbin ɗalibai ba wata hukuma ba, UniAbuja ta yi Martani ga JAMB
"Matar ta fito cikin fushi ta tambayeni, meyasa ka tsayar damu? Kafin in bata amsa sai kawai naji ta mareni a fuskata. Bance mata komai ba sai na tafi wajen mijinta nace mishi, Inason matar nan ta mareka kamar yadda ta mare ni."
"Wannan ɗaya ne daga cikin ƙalubalen dana fuskanta. Akwai cin mutunci da yawa da mutane suka min ina kan aikina amma bana nuna musu fushina."
"A matsayina na ma'aikaci dole in rinka fuskantar irin waɗannan matsaloli musamman kasancewa ta jami'in ɗan sanda." injishi.
A wani labarin kuma PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi
Jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga hukumar tsaro ta DSS data gayyaci ministan sadarwa, Isa Pantami, yazo ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.
Jam'iyyar tace ta damu matuƙa saboda ma'aikatar da Pantami ke rike da ita babbar ma'aikata ce dake ɗauke da muhimman bayanai.
Asali: Legit.ng