Bincike: Mafi yawancin Gwamnonin dake kan madafun iko sun fito ne daga wannan jami'ar

Bincike: Mafi yawancin Gwamnonin dake kan madafun iko sun fito ne daga wannan jami'ar

- A binciken da aka gudanar a hukumance ya nuna cewa a duk cikin gwamnoni biyar ɗaya daga cikinsu ya fito ne daga wannan jami'ar

- Jami'ar ta kafu tun shekaru 58 da suka gabata, tana da faɗin ƙasa da yakai hekta 7,000 kuma ta ƙunshi sashin karatu 106.

- An saka ma makarantar sunan Firimiyan arewa, Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, wanda a zamanin mulkinsa ne aka gina jami'ar

Jami'ar arewa, Ahmadu Bello University (ABU) dake Zaria, jihar Kaduna, tafi kowacce jami'a samar da gwamnoni a faɗin ƙasar nan, kamar yadda wani bincike da Premium Times ta gudanar a hukumance ya nuna.

Wani bincike da akayi akan tarihin karatunsu a hukumance ya nuna cewa rabin gwamnoni 36 na ƙasar nan sun yi karatunsu na digirin farko a jami'o'i guda uku na ƙasar nan, yayin da biyu daga cikin gwamnonin sukayi karatun digirinsu na farko a kasar waje.

KARANTA ANAN: Watan Ramadan: Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

ABU

Bakwai daga cikin gwamnonin yanzu sun yi karatun digirin farko ko na biyu a jami'ar ABU, an saka mata sunan firimiyan arewa, Ahmadu Bello, wanda a ƙarƙashin mulkinsa ne aka samar da jami'ar a jamhuriyar farko.

Gwamnonin da suka yi karatu a makarantar sun haɗa da, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Simon Lalong na Plateau, Badaru Abubakar na Jigawa, Inuwa Yahaya na Gombe, Nasir Elrufa'i na Kaduna, Darius Ishaku na Taraba da kuma Yahaya Bello na Kogi.

Biyar daga cikin gwamnonin bakwai sun yi karatun digirin su na farko a jami'ar a fannin lissafin kuɗi. Amma Elrufa'i da Ishaku sun yi na farko dana biyu a fannin zane-zanen gini.

Mr. Bello wanda ya fara karatun manyan makarantun gaba da sakandire a Foli ta jihar Kaduna, yayi karatun digirinsa na biyu a ABU.

Jami'ar ta kai shekaru 58 da kafuwa, wacce akafi sani da Jami'ar arewacin Najeriya, tana da faɗin ƙasa da yakai hekta 7,000. Kuma ta ƙunshi sasshi 106, hakan yasa ta zama ɗaya daga cikin makarantun da suka fi girma a kasashen yankin saharan Africa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, kashi ɗaya cikin uku na ministocin ƙasar nan daga jami'ar suka fito.

Bincike: A duk gwamnoni Biyar na yanzu, ɗaya daga Cikinsu Ɗalibin wannan makarantar ne
Bincike: A duk gwamnoni Biyar na yanzu, ɗaya daga Cikinsu Ɗalibin wannan makarantar ne Hoto: myschoolgist.com
Asali: UGC

UNILAG

Jami'ar Lagos (UNILAG), wacce take ma kanta kirari da 'Zaɓin farko' itace jami'a ta biyu wajen fitar da gwamnonin ƙasar nan.

Bincike ya nuna cewa UNILAG itace jami'a ta biyu dake da adadi mafi yawa na ministocin dake ci yanzun. Wannan na nufin ABU da UNILAG, su keda mafiyawan cin ministoci da gwamnonin dake ci a wannan gwamnatin.

Shida daga cikin gwamnonin yanzun sun yi karatun digirin farkon su ne a UNILAG, biyu daga cikinsu sun koma sun yi digiri na biyu a jami'ar.

Gwamnonin da suka halarci UNILAG sun haɗa da; Willie Obiano na Anambra, Babajide Sanwo-Olu na Lagos, Emmanuel Udom na Akwa Ibom, Kayode Fayemi na Ekiti, Gboyega Oyetola na Osun da kuma Seyi Makinde na Oyo.

KARANTA ANAN: Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed

UNIMAID

Jami'ar Maiduguri (UNIMAID) ta samar da biyar daga cikin gwamnonin dake mulki a yanzun, waɗanda mafi ƙaranci sun yi karatun digirin su na farko a jami'ar.

Yayin da gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum, yayi karatun digirinsa na biyu a makarantar, Sauran gwamnoni huɗun sunyi digirin su na farko ne a jami'ar.

Gwamnan Abia, Chikezie Ikpeazu, da gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, sun yi karatun digirinsu na farko dana biyu a UNIMAID.

UI da sauran jami'o'i

Jami'ar dake bin waɗancan ukun da suka gabata itace jami'ar Ibadan (UI), jami'ar ta yaye huɗu daga cikin gwamnonin ƙasar nan.

Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) ta samar da uku daga cikin gwamnonin yanzun, yayinda jami'ar Usman Ɗan-Fodio dake Sokoto (UDUS) da jami'ar Jos (UNIJOS) suke da gwamnoni biyu kowacce.

Jami'ar Najeriya, jami'ar Patakwal, jami'ar Bayero Kano, jami'ar jihar Enugu, jami'ar jihar Benuwai, jami'ar jihar Rivers, da kuma jami'ar fasaha dake Owerri, kowacce daga cikinsu nada gwamna ɗaya.

Yayin da 10 daga cikin gwamnonin suka yi karatun digirinsu a ƙasar waje. Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da na Ogun, Dapo Abiodun, sune kaɗai sukayi dukkan karatun su na manyan makarantun gaba da sakandire a ƙasar waje.

A wani labarin kuma Sufetan Yan sanda na ƙasa ya roƙi a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin daƙile dukkan matsalolin tsaro

Sufetan yan sanda na riƙo, Usman Alƙali Baba, ya buƙaci a ƙara ma hukumar yan sanda kuɗi domin su ƙara ƙaimi wajen sauke nauyin dake kansu na yaki da laifuffuka.

IGP ya bayyana haka ne a wata ziyara ta musamman da ya kaima kakakin majalisar wakilai domin nuna godiyarsa bisa ɗumbin goyon bayan da majalisa ke baiwa hukumarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel