Najeriya na tarwatsewa farfesoshi na iya komawa aiki a gidan Burodi, Lai Mohammed
- Minista Lai Mohammed ya gargadi masu fada aji a Najeriya kan batun wargajewar Najeriya
- Ya bayyana cewa, da yawan manyan mutane zasu shiga matukar wahala idan kasar ta watse
- Ya kuma siffanta cewa, ta yiwu farfesoshi su shiga tarkun aiki a gidan burodi a kasahen waje
Lai Mohammed, Ministan yada labarai da al’adu, ya ce yana da kyau manyan Najeriya su fahinci ci gaba da kasancewar Najeriya kasa daya, TheCable ta ruwaito.
Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da yake gabatarwa a wani shirin hira da jaridar NAN, NAN Forum.
Ministan ya zargi manyan mutane da ruruta wutar wargajewar kasar, kuma ya yi gargadin cewa za su dauki mafi girman munin sakamako idan Najeriya ta rabu.
A cewarsa, wasu manyan mutane da suka kai matsayin farfesa ana iya barinsu ba tare da wani zabin da ya wuce yin aiki a gidajen burodi a makwabciyar kasar Togo don kawai su rayu.
KU KARANTA: An kame 'yan bindiga masu tura wasikun barazana ga mutane a Adamawa
“Kalubalenmu ya fi yawa ga masu fada aji, ba wai talakawa ba. Ku je zuwa kauyuka a Najeriya a yau, za ku ga ‘yan Najeriya daga kabilu daban-daban, al’adu da addini suna zaune tare cikin lumana,” inji shi.
“Ya kamata masu fada aji su shige gaba wajen don tabbatar da hadin kan kasar. Amma lokacin da masu fada aji suka fara da'awar kiyayya na kabilanci, mutane suna gaskata su saboda suna tunanin sun fi sani.
“Najeriya na dauke da 70% na al’ummar Yammacin Afirka, kuma idan Najeriya za ta wargaje a yau, za mu mamaye Jamhuriyar Benin, Togo, Nijar da sauran kasashe makwabta.
“Masu fada aji za su sha wahala matuka saboda wasu furofesoshi za su iya komawa aiki a gidajen burodi a Togo don tsira da rayuwarsu kawai. Mun ga abin da ya faru lokacin da 'yan Liberiya suka zo nan lokacin yakin basasarsu.
“Yana daga cikin damarsu karan-kanasu su yi aiki don gyara Najeriya. Yawancinsu suna da fasfo fiye da daya - Na Amurka, Biritaniya, Turai - kuma a farkon tashin hankali, zasu gudu."
KU KARANTA: Duk 'ya'yana a makarantar gwamnati suke, ba ma son a sace su, in ji wani ministan Buhari
A wani labarin, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce mutanen da ke neman ballewa su ne zasu zama na farko da za su tsere daga kasar idan irin wannan hargitsi ya haifar da rikici.
Mohammed, wanda ya yi magana a ranar Lahadi, 18 ga Afrilu, a jihar Legas lokacin da ya bayyana a shirin gidan rediyon Bond FM, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su saurari masu kira ga ballewa, The Cable ta ruwaito.
Ya ce: "Wadanda ke goyon bayan rabuwa da ballewa su ne za su fara gudu yayin da wata matsala ta biyo baya.
Asali: Legit.ng