An kame 'yan bindiga masu tura wasikun barazana ga mutane a Adamawa

An kame 'yan bindiga masu tura wasikun barazana ga mutane a Adamawa

- 'Yan sanda sun yi nasarar kame wasu bata-gari dake wa mutane barazana da aika wasikun barazana

- An kame su ne a jihar Adamawa yayin da suka aika da wasikun barazana cewa zasu sace wasu mutane

- Rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa ta bayyana cewa, za ta gurfanar dasu a gaban kotu nan kusa

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Adamawa ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da satar mutane, sun kwato bindigogi guda uku, wayar hannu, layukan waya, wasikun barazana da kudi N86,000, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun labari daga majiya.

“A ranakun 9/4/2021 da 11/4/2021, jami’an rundunar da ke hade da sashin Gombi, sun karbi korafi daga mutanen gari, mazauna kauyukan Wuro Garba da Lugga na karamar hukumar Hong, cewa sun samu wasiku daban-daban da ke barazanar su biya N1m kowannensu ko kuma a sace su.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya

An kama wasu da ake 'yan bindiga ne tare da wasikun barazana a Adamawa
An kama wasu da ake 'yan bindiga ne tare da wasikun barazana a Adamawa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Bincike ya kai ga cafke Adoneja Dauda, ​​mai shekaru 30, mazaunin kauyen Hubbare, karamar hukumar Maiha a matsayin babban wanda ake zargi wanda ya aiko da wasiku na barazanar don karbar talikan jama'a.

“Kafin a kamashi, wanda ake zargin ya amshi kudi N150,000 daga wani Alhaji Dauda Hazzan, mazaunin kauyen Barkaji, karamar hukumar Hong tare da tsoratar da shi don sace shi.

“Hakanan, rundunar ta sake samun wata nasara ta hanyar cafke Musa Saidu mai shekaru 26, Manu Hussein mai shekaru 25 da Hammadu Bello mai shekaru 22. Duk mazaunan kauyen Garwayel, Hong, karamar hukumar Hong.

“Wadanda ake zargin a wasu lokuta a cikin watan Maris, 2021 sun yi garkuwa da Alhaji Yahaya Buba, Alhaji Sure da Alhaji Muhammed Bello duk na kauyen Konto, karamar hukumar Gombi,” in ji shi.

Kakakin ya bayyana cewa rundunar ta zurfafa binciken leken asiri domin karfafa tsaro a jihar.

Ya kuma ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

KU KARANTA: An yi kutse a shafin Facebook na Dr Pantami biyo bayan wani sharhi da ya yi

A wani labarin, 'Yan sandan Najeriya sun hallaka 'yan bindiga 30 bayan da wasu gungun 'yan ta'adda suka afkawa kauyuka Hudu a arewa maso yammacin kasar, in ji 'yan sanda a ranar Talata.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar ta Zamfara Mohammed Shehu ya fada a cikin wata sanarwa cewa, akalla mazauna kauyuka 10 aka kashe a wasu hare-hare daban-daban, kafin 'yan sanda su mai da martani kan 'yan bindigan.

Wasu gungun 'yan ta'adda dauke da muggan makamai wadanda aka fi sani da "'Yan bindiga" sun zama manyan masu kalubalantar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya, suna addabar kauyuka tare da yin garkuwa da mutane da dama tare da karbar kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel