Duk 'ya'yana a makarantar gwamnati suke, ba ma son a sace su, in ji wani ministan Buhari

Duk 'ya'yana a makarantar gwamnati suke, ba ma son a sace su, in ji wani ministan Buhari

- Karamin ministan ilimi na Najeriya ya koka kan yawaitar sace dalibai a arewacin Najeriya

- Ya bayyana cewa, shi ma dukkan 'ya'yansa na karatu ne a makarantun gwamnati a kasar

- Ya nuna jimami tare da nuna damuwa da yawaitar sace-sacen a wani bidiyon hirarsa da gidan talabijin

Karamin ministan Buhari a hukumar ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya koka kan yadda lamarin yake kara yawaita.

Ya bayyana cewa, gwamnati na jin zafin yawaitar satan, ya kuma bayyana cewa shi da kansa ya na da 'ya'ya a makarantar gwamnati.

Ministan ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a jiya Talata 20 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Tarihin Ibnu Battuta mai daukar hankali, daya daga cikin matafiyan da suka zagaye duniya

Ministan Buhari ya koka kan yawan sace dalibai, ya ce 'ya'yansa a makarantar gwamnati suke
Ministan Buhari ya koka kan yawan sace dalibai, ya ce 'ya'yansa a makarantar gwamnati suke Hoto: icirnigeria.org
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta gano ministan yana bayyana rashin jin dadinsa tare da taya iyayen da aka sace 'ya'yansu jimami yana mai cewa:

"Ina cikin damuwa kamar yadda iyaye na gaba suke ciki(game da rashin tsaro a makarantu). Dukkan ’ya’yana suna makarantun gwamnati a Najeriya".

Lamarin sace dalibai a Najeriya, musamman Arewa maso Yammaci yana kara yawaita. A yau ne aka sace wasu adadi na daliban wata jami'a mai zaman kanta a jihar Kaduna.

Rundunar 'yan sanda ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, in da ta bayyana cewa tana kan bincike akai.

Ba wannan ne karo na farko da aka sace dalibai a jihar ba, a baya-bayan nan an sace daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji na jihar ta Kaduna.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga sun sace daliban da ba a san adadin su ba daga Jami’ar Green Field da ke jihar Kaduna.

Jaridar TheCable ta fahimci cewa 'yan bindigan sun farma makarantar ne da tsakar daren Talata. An ce sun bude wuta ne don tsoratar da mazauna yankin kafin su sace wasu daliban.

Jami’ar mai zaman kanta tana kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuka a karamar hukumar Chikun, daya daga cikin wuraren da ‘yan bindiga suke a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel