Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu tsere

Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu tsere

- Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya mayar da martani game da hargitsi daga masu fatutukar ballewar

- Ministan ya bayyana dalilin da ya sa ballewar ba zai amfani kasar ba matukar ba mafita zaa nemo ba

- Ministan ya kuma bayyana wasu matsalolin da kasar ke fuskanta da ya kamata a mayar hankali akai

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce mutanen da ke neman ballewa su ne zasu zama na farko da za su tsere daga kasar idan irin wannan hargitsi ya haifar da rikici.

Mohammed, wanda ya yi magana a ranar Lahadi, 18 ga Afrilu, a jihar Legas lokacin da ya bayyana a shirin gidan rediyon Bond FM, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su saurari masu kira ga ballewa, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 6 a jihar Neja

Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu gudu
Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu gudu Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Ya ce: "Wadanda ke goyon bayan rabuwa da ballewa su ne za su fara gudu yayin da wata matsala ta biyo baya.

"Bai kamata mu saurare su ba saboda yawancinsu suna da fasfot hudu na wasu kasashen."

Ministan ya dage cewa ballewa ba shi ne mafita ga kalubalen da ke fuskantar Najeriya ba.

A cewar jaridar Vanguard, Mohammed ya nuna cewa rikice-rikice a kasar kamar kabilanci, ayyukan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da rikicin manoma da makiyaya ba sabon abu bane.

Ya kuma bayyana cewa maimakon kira ga rabuwa, dole ne ‘yan Najeriya su nemi hanyar da za a samo mafita mai dorewa. Ya ce: "Ba ku warkar da ciwon kai ta hanyar fille kan mara lafiya."

KU KARANTA: Kar ku zagi kowa a madadi na, Dr. Pantami yayi raddi kan zarginsa da ta'addanci

A wani labarin, A wani harin 'yan bindiga, akalla gidaje 50 ne suka kone tare kayan gona a wani sabon rikicin kabilanci a garin Nyuwar, na Jessu da ke jihar Gombe, The Punch ta ruwaito.

Ku tuna cewa an kashe mutane 19 tare da daruruwan gidaje da ba a san ko su waye suka lalata ba a rikicin Waja/Lunguda.

Wani shaidar gani da ido, Ily Maisanda, ya ce tuni mazauna garin suka tafi Yolde don tsare kansu, in da ‘yan bindigan suka yi amfani da wannan dama wajen kai sabon hari a Nyuwar ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel