CSOs sun buƙaci Buhari ya yi watsi da kiraye-kirayen sauke Pantami

CSOs sun buƙaci Buhari ya yi watsi da kiraye-kirayen sauke Pantami

- Hadakar Kungiyoyi Masu Kare Hakkin Bil'Adama, CSOs sun yi kira da Shugaba Buhari ya yi watsi da masu neman a sauke Dr Pantami

- A cewar kungiyoyin, wasu marasa kishin kasa ne da ba su son zaman lafiya da tsaro suka dauki nauyin abin saboda a dakatar da rajistar NIN

- Kungiyoyin sun ce Ministan na Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani mutum ne mai nagarta da ke kawo sauye-sauye masu amfani a kasar

Hadakar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'Adama da Tabbatar da Mulki na Gari ta ce wasu ne suka dauki nauyin kiraye-kirayen da ake yi a kafafen sada zumunta na neman sauke Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami da nufin kara lalata harkar tsaro a kasar.

Hadakar ta ce wadanda suka dauki nauyin abin suna cigaba da samun riba daga kallubalen rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

CSOs sun buƙaci Buhari ya yi watsi da kiraye-kirayen sauke Pantami
CSOs sun buƙaci Buhari ya yi watsi da kiraye-kirayen sauke Pantami. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

A jawabin da ya yi a Legas a ranar Talata 20 ga watan Afrilu, jagoran hadakar, Kwamared Declan Ihekaire, ya ce sun damu kan ganin yadda ake ci cigaba da neman sai Pantami ya sauka.

Hadakar ta bayyana Pantami a matsayin mutum mai nagarta da basira kuma daga cikin mutane masu muhimmanci a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ihekaire ya ce tilas ta sa suka fito domin yin Allah wadai da bata sunan da wasu marasa kishin kasa da ke amfana da rashin tsaro ke yi wa Dr Pantami da masu adawa da batun rajistan NIN wanda zai taimakawa kasar wurin dakile laifuka da samar da tsaro.

KU KARANTA: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

Har wa yau, kungiyoyin sun ce sun gamsu da gaskiya irin ta Dr Isa Pantami inda ya amsa cewa a baya ya furta wasu maganganu da ake yi wa kallon goyon bayan kungiyoyin ta'addanci amma tuni girma ya zo masa kuma ya sauya tunaninsa.

Don haka kungiyar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da masu kiraye-kirayen ya sauke Dr Pantami kuma kada ya bari marasa kishin kasa su lalata masa gwamnati.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel