An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

- Wasu sojoji da aka kama kan taimakon Boko Haram sun tona fararen hula da suke aiki da su

- Kimanin 20 da aka kama a Borno kuma yayin musu tambayoyi ne suka ambaci fafaren hulan da suka aiki tare suma an kamo su

- Amma Kakakin rundunar sojojin Nigeria, Mohammed Yerima ya ce ba shi da masaniya kan kama sojojin 20 da fararen hulan

Wasu sojoji da aka kama yayin binciken masu daukan nauyin yan Boko Haram sun bayyana sunayen wasu fararen hula da suke aiki tare da su a cewar majiyoyi, rahoton Daily Trust.

An kama sojojin ne bayan bincike mai zurfi da aka yi kan alakar da ke tsakanin yan Boko Haram da jami'an sojoji, da suka taimaka musu wurin zagon kasa kan yakin da ake yi na kawo karshen ta'addanci a Nigeria.

An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram
An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike kan wadanda suke daukan nauyin yan ta'adda da masu hada kai da Boko Haram.

Wani babban jami'in tsaro mai binciken sirri ne ka jagorantar binciken tare da babban janar na soja d wasu ma'aikata daga hukumomin binciken sirri.

Majiyoyi da dama sun sanar da majiyar Legit.ng cewa Hukumar Binciken Sirri na kasa, DIA tare da hadin kan DSS, NFU da babban bankin kasa CBN ne ke binciken.

A halin yanzu an kama sojoji 20 da ake zargi da hannu cikin lamarin kuma suna tsare a Borno.

"An kama kimanin 20 daga cikinsu suna tsare a Borno. A yayin binciken sun bada bayanai masu yawa ciki har da sunayen wasu fararen hula da suke aiki tare da su inda suka aka kama su," majiya ta shaidawa Daily Trust.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Nijar a Aso Rock

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar sojoji, Manjo Jana Mohammed Yerima ya ce ba shi da masaniya kan kama sojoji da ake zargi suna hada kai da yan Boko Haram.

Ya kuma ce hukumar yan sandan farar hula, DSS, ya kamata a yi wa wannan tambayar domin su ke kula da batutuwan da suka shafi kama masu daukan nauyin ta'addanci.

Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS, a yayin da aka tuntube shi a ranar Juma'a ya ce zai yi bincike kafin ya yi tsokaci kan batun. Amma bai bada bayanin ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton.

Bai kuma amsa kira da sakon kar ta kwana da aka yi ta tura masa ba.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel