Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika
- Iyalan Sheikh Shehu Mai'Annabi da masu garkuwa suka sace tare da iyalansa sun ce suna cikin fargaba
- Hakan na zuwa ne yayin da wa'adin da masu garkuwa suka basu don biyan fansa ya kusa cika
- Malam Isiyaku, babban dan Mai'Annabi ya ce masu garkuwar sun ce za su kashe malamin da sauran dalibansa idan ba a biya kudin ba bayan cikar wa'adin
Iyalan fitaccen malamin addinin musulunci na Kano, Sheikh Abdullahi Shehu Mai’Annabi, da aka sace tare da kaninsa da dalibansa 11 a hanyarsu ta zuwa Zamfara, kwanaki 40 da suka shude sun shiga damuwa a yayin da wa'adin da masu garkuwa suka basu na biyan fansa ya kusa cika.
Masu garkuwar sun bawa iyalan wa'adi daga 12 zuwa 20 ga watan Afrilun 2021 su kawo Naira miliyan 5 domin ya cika Naira miliyan 10 da suka nema kafin su sako wadanda suka yi garkuwar da su, Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: An cafke wasu mutum biyu da ke yi wa ƴan bindiga aikin 'likitanci' a Kaduna
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yadda masu garkuwar suka fada wa iyalan su tafi su dauki gawar mutum hudu da suke kashe bayan an biya su Naira miliyan 5.
Malaman Isiyaku, babban dan malamin ya ce sun shiga mawuyacin hali tun bayan sace mahaifinsu a watan Maris.
Ya ce masu garkuwar sun gargade mu cewa za su kashe dukkan wadanda suka rike da su idan har an gaza basu kudin fansar da suka nema zuwa ranar 20 ga watan Afrilu.
"Sun ce idan ba mu samo kudin ba kafin ranar, za su kira mu su fada mana inda za mu dauki gawarwakin wadanda suka sace."
Ya ce masu garkuwar sun bashi dama ya yi magana da mahaifinsa domin ya tabbatar yana da rai amma a halin yanzu ba su da kudin da ake nema hasali ma iyayen Almajiran ne suka nema Naira miliyan 5 da aka biya da farko.
KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun ji 'ba daɗi' a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa
Da farko masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 15 sannan daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 10.
Isiyaku ya ce shi da mahaifiyarsa sun yi kokarin ganin kwamishinan yan sandan Kano domin shigar da korafinsu amma ba su samu daman ganinsa ba hakan yasa suka rungumi kaddara.
Kakakin yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ba shi da masaniya a kan maganar a yayin da aka tuntube shi.
Asali: Legit.ng