Direbobi sun shiga yajin aiki saboda fashi da makami da garkuwa a Zamfara
- Direbobin mota a jihar Zamfara sun shiga yajin aiki saboda yawan fashi da sace mutane a titin Gusau zuwa Dansadau
- Shugaban kungiyar direbobi na kasa, NURTW, na Dansadau, Isihu Ticha ne ya bayyana hakan
- Ticha ya ce an kashe kimanin direbobi uku a baya bayan nan a titin sannan an kwace babura da suka kai 16
Direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aiki saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.
Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.
DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak
Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.
An sace direbobi uku a titin a baya bayan nan sannan yan bindiga sun kwace babura guda 16 cikin mako daya.
"Kusan kowanne rana sai an yi fashi ko garkuwa da mutane a titin. Ranar Juma'a da ta gabata an bindige wani direba da ke dauke da amarya da wasu baki har lahira, an kuma sace amaryar da bakin a kusa da Mashaya Zaki, wuri mai hatsari sosai mai nisan kilomita 15 daga garin Dansadau. Motar ta yi kundinbala amma hakan bai hana su sace mutanen da ke ciki ba," in ji Ticha.
"Kafin wannan, an kashe a kalla direbobi uku da ke bin titin. Kazalika, an sace direbobi hudu inda suka shafe kimanin kwanaki 40 a tsare. Wadanda suka sace su ba su tuntube kowa ba don haka ba mu san ko suna da rai ko sun mutu ba. Muna cikin mawuyacin hali a nan," in ji shugaban na NURTW.
KU KARANTA: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta
Ya kara da cewa akwai sojoji a titin amma baya tunanin adadin su ya wadata ta yadda za su samar da tsaro don haka ya yi kira ga mahukunta a ajiye sojoji a wuraren da ke da hatsari sosai.
A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.
Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.
Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.
Asali: Legit.ng