Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka, Walter Mondale ya mutu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka, Walter Mondale ya mutu

- Allah ya yi wa tsohon mataimakin shugaban Amurka, Mondale rasuwa

- Mondale ya rasu a gidansa da ke Minneapolis yana da shekaru 93 a duniya

- Mondale ya rasa matarsa Joan a 2014 sannan yarsa Eleanor ta rasu a 2011

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Mr Walter Fredrick "Fritz" Mondale ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Mr Mondale wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa karkashin gwamnatin Shugaba Jimmy Carter ya rasu ne yana da shekaru 93 a cewar mai magana da yawun iyalinsa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka Walter Mondale ya mutu
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka Walter Mondale ya mutu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

Marigayin ya taba neman takarar shugaban kasa a 1984 amma bai yi nasara ba.

Majiyoyi sun ce ya rasu ne a gidansa da ke Minneapolis tare da yan uwansa duk da cewa ba a sanar da abin da ya yi ajalinsa ba.

"Lokaci ne ya yi. Na kosa in tafi in hadu da Joan da Eleanor," Mondale ya ce a cikin wata sanarwar da ya rubuta ga ma'aikatansa kuma aka fitar bayan rasuwarsa.

"Kafin in tafi, ina son in sanar da ku irin muhimmancin da kuke da shi a wuri na."

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun ji 'ba daɗi' a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa

Joan tsohuwar matarsa ce da ta rasu a shekarar 2014 sannan Eleanor yarsa ce da ta rasu a shekarar 2011 tana da shekaru 51 a duniya.

Mondale ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa karkashin Jimmy Carter daga shekarar 1977 zuwa 1981.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel