'Yan Boko Haram sun ji 'ba daɗi' a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa
- Rundunar sojojin Nigeria ta ce dakarunta sun dakile harin da Boko Haram suka kai a Dikwa a jihar Borno
- Rundunar sojojin ta ce dakarunta sun kashe yan Boko Haram da dama tare da lalata musu makamai da motoci
- Mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, Manjo Janar Mohammed Yerima ne ya bada sanarwar
Dakarun sojojin Nigeria, a ranar Lahadi sun dakile yunkurin da yan Boko Haram suka yi na kwace iko a garin Dikwa, hedkwatan karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
Sanarwar ta mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, Mohammed Yerima ya fitar a Twitter ta ce yan ta'addan da dama sun mutu a yayin harin da suka yi yunkurin kai wa.
Yan ta'addan sun dade suna kai hari a garin Dikwa a shekarun baya-bayan nan suna addabar mutanen garin.
DUBA WANNAN: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram
Harin baya bayan shine wanda suka kai kimanin wata daya da ya wuce suka sace ma'aikatan jin kai guda bakwai.
A yayin harin, sun kuma kona ofishin ma'aikatan jin kan, suka lalata wasu kayayyakin gwamnati da asibiti mallakar wata kungiyar taimakon mutane mai zaman kanta.
Sanarwar ta ce yan ta'addan sun rasa mayakansu da yawa ciki har da manyan kwamandojinsu da kayayyakin yaki.
Amma rundunar sojojin ba ta fayyace adadin yan ta'addan da sojojin suka halaka ba yayin harin.
Sanarwar ta ce, "Dakarun Operation Lafiya Dole da ke atisayen Tura ta kai bango a Dikwa da Gulumba Gana tare da taimakon sojojin sama sun halaka yan Boko Haram da dama wadanda suka yi yunkurin kwace wasu sassa na Dikwa, hedkwatar karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
"Yan ta'addan da dama da suka shigo garin a cikin motocci masu bindiga 12 sun kai hari a garin na Dikwa a ranar Lahadi 18 ga watan Afrilu dab da lokacin da mutane ke shirin shan ruwa.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Nijar a Aso Rock
"Sojojin da suka fatattaki yan bindigan tunda farko sun koma hedkwatarsu ta Gulumba Gana domin bawa jiragen yaki daman yi wa yan ta'addan ruwan wuta. Da safiyar ranar Litinin 19 ga watan Afrilun 2021 sojojin sun mayarwa yan ta'addan martani suka sake kwace hedkwatarsu da ke Dikwa."
"Yan ta'addan sun rasa mayakansu da makamansu da dama a yayin da suke kokarin tserewa cikin wadanda suka mutu har da manyan kwamandojinsu sakamakon luguden wuta ta sama da kasa da sojojin suka yi musu."
Yerima ya ce a halin yanzu sojojin suna sintiri a garin na Dikwa suna nazarin irin barnar da suka yi wa yan ta'addan.
A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.
Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.
Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.
Asali: Legit.ng