Da duminsa: Gobarar tanka ta sake ƙona gidaje da dama a Benue

Da duminsa: Gobarar tanka ta sake ƙona gidaje da dama a Benue

- Wata tanka dauke da man fetur ta sake fadi ta yi gobara a jihar Benue

- Hakan na zuwa ne bayan an yi wani gobarar tankar a jihar a ranar Lahadi

- Mr John Ikwulono, shugaban karamar hukumar Agatu ya tabbatar da afuwar gobarar

Wata tanka ta sake faduwa a jihar Benue kwanaki biyu bayan wata tankar ta fadi ta yi gobara a Oshigbudu a karamar hukumar Agatu na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Idan za a iya tunawa mutane 12 ne suka riga mu gidan gaskiya a gobarar tankar ta ranar Lahadi a Oshigbudu inda gidaje da dama suka kone.

Da duminsa: Gobarar tanka ta sake kone gidaje da dama a Benue
Da duminsa: Gobarar tanka ta sake kone gidaje da dama a Benue. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sheikh Mai'Annabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

Wannan gobarar na yanzu, a cewar majiyoyi, ya faru ne a safiyar ranar Talata kusa da wurin da gobarar na baya ya faru.

Mataimakin shugaban karamar hukumar, Mr John Ikwulono ya tabbatar da afkuwar gobarar sannan ya ce ba a rasa rai ba sai dai wasu gidaje sun kama da wuta.

Majiyar Legit.ng ta ce kusa da ofishin yan sanda gobarar ta faru.

"Gidaje da dama sun kone. Duk da cewa ba mu kai ga tantance adadin gidajen ba, sai dai ba su kai yawan gidajen da suka kone a gobarar ranar Lahadi ba.

"Amma mun gode wa Allah babu wanda ya rasa ransa, Direban motar ya tsere amma an kama kwandasta an mika shi ga yan sanda. An fada min cewa tankar da ke dauke da man fetur ta fadi ne misalin karfe 4 zuwa 5 na asubahi" Ikwulono ya ce.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun ji 'ba daɗi' a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa

Mataimakin shugaban karamar hukumar ya ce mutane sun yi ta amfani da ruwa da sabulu domin kashe gobarar.

Sai dai hukumar kiyayye haddura, FRSC, na Benue ta tabbatar da cewa gidaje biyu ne kacal suka kone sakamakon gobarar tankar a Agatu.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel