Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS

Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS

- Wani tsohon Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS yace matuƙar Najeriya ta cigaba da tafiya a haka to zaɓen 2023 ma bazai yuwu ba

- Tsohon Daraktan yace yakamata gwamnati ta farka, ta magance matsalar tsaro tun kafin lokacin zaɓen ya yi

- Daraktan ya goyi bayan kiraye-kirayen da akeyi na sake fasalta ƙasar nan, a cewarsa hakan zai taimaka wajen warware wasu matsalolin

Wani tsohon Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Mike Ejiofor, ya yi gargaɗin cewa zaɓen dake ƙaratowa na 2023 bazai yuwu ba sabida ƙara taɓarɓarewar da harkar tsaro ke yi a ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti

Lokacin da yake jawabi a wata tattaunawa da Channels TV cikin shirin 'Sunrise Daily', Ejiofor ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar.

Tsohon Daraktan yace Matuƙar ba'a daƙile matsalar nan kafin zaɓen 2023, kuma ba'a warware dukkan ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a yankuna daban-daban na ƙasar nan ba, to babu ta yadda za'ayi zaɓe ya yuwu a wannan yanayin.

Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS
Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Mine Ejiofor ya ce:

'Idan bamuyi da gaske mun magance matsalar nan ta tsaro ba, bamu warware matsalar ba a dukkan yankunan da abun ya shafa a ƙasar nan, to ina mai tabbatar muku bazai yuwu a gudanar da zaɓe ba."

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

"Za'a samu hargitsi da tarzoma a ƙasar nan, yakamata mu yi duk abinda ya dace mu warware matsalolin nan kafin shekarar 2023."

"Mu ajiye maganar zaɓe a gefe guda, matuƙar muka cigaba da tafiya a haka to zaɓen ma bazai yuwu ba."

Duk da jerin gwanon matsalolin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta, Ejiofor ya goyi bayan kiran da ake na sake zama domin gyara fasalin ƙasar nan.

Ya ce wannan aikin na gayaran fasalin ƙasa zai taimaka sosai wajen ganin an warware da yawa daga cikin matsalolin.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram.

Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci.

Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262