PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

- Jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga hukumar tsaro ta DSS data gayyaci ministan sadarwa, Isa Pantami, yazo ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa

- Jam'iyyar tace ta damu matuƙa saboda ma'aikatar da Pantami ke rike da ita babbar ma'aikata ce dake ɗauke da muhimman bayanai

- Kakakin jam'iyyar PDP ne ya bayyana haka ranar Lahadi, inda ya ce sun tsoron ministan ya shigo da wasu abubuwa da basu dace ba a rijistar NIN da ake cigaba da yi a yanzun

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, ta roƙi hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da su gaggauta gayyatar ministan sadarwa, sheikh Isa Pantami, domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na goyon bayan qungiyoyin ta'addanci.

KARANTA ANAN: Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro

Hakanan kuma jam'iyyar ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara a kan ministan, tace yakamata ya kula sosai da wannan lamarin.

PDP ta bayyana matsayarta ne a wani jawabi data fitar ɗauke da sa hannun kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan , ranar Lahadi kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kola Ologbondiyan yace:

"Jam'iyyar mu ta damu matuƙa da lokacin da ake ɗauka kan wannan lamarin da kuma jayayya da ministan sadarwa, wanda keda ajiyayyun bayanan gwamnati, da bayanan wasu ɗaiɗaikun mutane masu ƙima."

"PDP ta damu matuƙa da zargin da mutane ke masa, kuma muna gudun kada ministan ya yi abinda bai dace ba wajen baiwa wasu daba yan ƙasa ba dama suzo su mamaye rijistar NIN ɗin da ake yi yanzun, su zama yan ƙasa."

PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan Ya amsa Tambayoyi
PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan Ya amsa Tambayoyi Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Buhari bai kasa Cika alƙawurransa ba, Yana hakuri ne da wautar wasu mutane, Inji Gwamna Masari

"Jami'iyyar PDP na kira ga DSS su gudanar da bincike kan zarge-zargen, wanda ya jawo cece-kuce da tsoro sosai musamman ma sabida ƙaruwar hare-haren yan bindiga da sauran ayyukan ta'addanci aƙasar nan."

Sai dai a ƙarshen makonnan minista Pantami yace bai taɓ zama mai tsattsauran ra'ayi ba kuma shi baya kan wasu maganganu da yayi a baya.

Ya kuma ce babu wani malamin addinin musulunci a baya ko a yanzun da ya ƙalubalanci ayyukan Boko Haram kamar shi.

Pantami ya faɗi haka ne a lokacin gudanar da tasirin watan Ramadana da yake gudana a masallacin An-Noor, Abuja.

A wani labarin kuma PDP ta hurowa Shugaba Buhari Wuta, Ta nemi ya sallami Sheikh Pantami

Babbar jam'iyyar adawa PDP ta hurawa shugaba Buhari wuta kan ya sallami ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami.

Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Uche Secondus, shi ne ya yi kira ga shugaban da ya sallami ministan matuƙar bai aje muƙaminsa da kansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262