Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro

Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro

- Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci

- Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'

- Ministan yace gwamnatin tarayya zata baiwa jin dadi da walwalar sojojin kulawa ta musamman

Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce nan bada jimawa ba gwamnatin tarayya zata fara ɗaukar sabbin sojoji a faɗin ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Buhari ya jajantawa Mutanen jihar Adamawa kan harin yan ta'adda, Ya ce ba za'a sake ba

Lokacin da yake jawabi a hedkwatar sojojin dake Maiduguri yayin da ya jagoranci shugaban tsaro CDS, General Lucky Irabor, da sauran shuwagabannin tsaro suka kai ziyara.

Magashi yace shirin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ganin ta kawo ƙarshen ta'addanci kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ministan ya ce babban makasudin wannan ziyara shine su ƙara ma rundunar soji ta 'Operation Lafiya Dole' ƙwarin gwuiwa akan yaƙin da suke yi.

Yayin da yake jawabi ga sojojin, Magashi ya bayyana musu shirin da gwamnati ke yi na ɗaukar sabbin sojoji domin rage musu ayyuka da yawa.

Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro
Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro Hoto: @GenMagashi
Asali: Twitter

Bashir Magashi yace:

"Ba da jimawa ba zamu ƙaddamar da ɗaukar sabbin sojojin da ofisoshi saboda mu ƙara yawan jami'an tsaron mu."

"Zamu kawo sabbin kayan aiki, sabbin dabarun yaƙi, waɗanda zasu amfaneku, zasu kara muku kwarewa akan wannan aiki da kukeyi. Mun bata lokaci sosai, yanzun shekaru 10 kenan ana wannan aikin."

KARANTA ANAN: Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari

"Akwai sauran wasu ayyukan da muke yi a sassan ƙasar nan, amma inada tabbacin idan aka baku kayan aikin da yakamata, zaku sa ƙasar mu alfahari."

"Munyi amanna daku, da horon da kuka samu, da kuma ƙwarewarku, munyi amanna zaku iya share Boko Haram gaba ɗaya kamar yadɗa kuke yi yanzun."

Ministan tsaron ya kuma bayyana ma manema labarai cewa gwamnati ta ɗauki jin daɗi da walwalar sojoji da matuƙar muhimmanci.

Ya kuma bada umarnin a rubuta masa duk wata matsala da rundunar ke fuskanta domin su duba kuma su fito da sabon tsari don magance su

A wani labarin kuma Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda

Ministan yace ya canza da yawa daga cikin waɗannan maganganun saboda ƙarin ilmi da kuma gogewa da yayi.

Ya ce a musulunci akwai irin waɗannan domin ko manyan malaman addinin da ake ji da su, irin su Imamu Malik sun yi fatawa kuma suka canza daga baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel