Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti

Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti

- Mutane 20 sun rasa rayukansu a wasu hare-haren ramuwar gayya da ya faru tsakanin yan bindiga da kuma jami'an Bijilanti a jihar Zamfara

- Mazauna yankin da kuma ma'aikatan Asibitin da aka ajiye gawarwakin sun tabbatar da rasa rayukan, amma sun nemi a sakaya sunan su

- Sai dai ba'a sami ko ɗaya daga cikin kwamishinan tsaron cikin gida ko kwamishinan yaɗa labaran jihar ba bare aji rahoton a hukumance

Aƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis da kuma Jumu'a a wani harin ramuwar gayya tsakanin yan Bindiga da yan Bijilanti a yankin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

KARANATA ANAN: Buhari ya jajantawa Mutanen jihar Adamawa kan harin yan ta'adda, Ya ce ba za'a sake ba

Mazauna yankin da kuma jami'an asibiti ne suka tabbatar da adadin ga wakilin jaridar Premium Times yayin da yakai ziyara yankin.

Mazauna garin sun bayyana cewa lamarin ya fara ne daga lokacin da yan bindigar suka kashe mutane uku a wani hari da suka kai Ruwan Tofa ranar Alhamis.

Bayan faruwar haka, sai jami'an bijilanti suka ƙaddamar da harin ramuwar gayya a kasuwar shanu dake Ɗansadau, inda suka kashe mutane 16 yan ƙabilar Fulani, suka bar mutum bakwai cikin mummunan rauni.

Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da jami'an Bijilanti daga gudanar da aiki a jihar saboda ƙorafin da jama'ar Fulani suka kai cewa jami'an suna kaima mutanen su hari ba gaira babu dalili.

Wani mazaunin garin, wanda ya roƙi a sakaya sunansa sabida yanayin tsaro yace, ɗaya daga cikin mutane uku da aka kashe a Ruwan Tofa ranar Alhamis, Sanusi Manu, ya kasance mamba ne a cikin tawagar yan Bijilanti.

Mutumin yace yan bindiga ne suka kashe mahaifin Manu, Alhaji Maiburkasa, shekaru bakwai da suka gabata.

Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti
Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya ce mutuwar jami'insu, Manu, shine yasa tawagar yan Bijilantin ƙaddamar da harin ramuwar gayya a kasuwar shanu dake Ɗansadau ranar Jumu'a da safe.

Amma a ranar Jumu'a da yamma, wasu da ake zargin yan bindiga ne suka sake kai sabon hari a Mai-Tukunya domin ɗaukar fansar abinda akai musu da safiyar ranar a kasuwa.

KARANTA ANAN: Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari

"Daga cikin waɗanda aka kashe a harin kasuwar akawai ɗaya daga cikin shuwagabannin Fulani, Barume Saulawa. Jami'an tsaro sun rako wasu makiyaya asibiti ranar asabar da safe domin su duba ragowar yan uwansu da aka kashe." inji wani ma'aikacin Asibitin.

Ma'aikacin ya nemi kada a bayyana sunansa saboda basu da damar yin magana da manema labari.

Jami'an tsaron sun bayarda gawarwakin waɗanda aka gane ga makiyayan, amma an bar wasu anan ba tare da angane yan uwansu ba wanda hakan ya nuna mutane da yawa sun mutu ko kuma sun bace a yayin harin da aka kai kasuwar.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun zargi jami'an tsaron yankin da suka ƙi yin komai domin kare harin ramuwar gayya da aka kai Mai-Tukunya ranar Jumu'a da yamma.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Abubakar Dauran, da kwamishina yaɗa labarai, Ibrahim Dosara, basu ɗaga waya ko suka dawo da amsar saƙonnin da aka tura musu ba, lokacin da aka nemi su yi jawabi a kan rahoton a hukumance.

Hakanan kuma, Shima mai magana da yawun yan sandan jihar, Muhammad Shehu, bai amsa kiran da aka masa da saƙonnin da aka tura masa a ranar Asabar da Lahadi.

A wani labarin kuma Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

Rundunar yan sandan jihar Enugu ta kama wata matashiyar mata da zargin kisan ɗan kishiyarta.

Matar da ake zargin ta amsa laifinta, amma tace ta yi haka saboda mijinta baya bata kulawa sam da ita da yayanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262