A karshe Isa Pantami ya magantu, ya bayyana dalilin da yasa ake alakanta shi da ‘yan ta’adda

A karshe Isa Pantami ya magantu, ya bayyana dalilin da yasa ake alakanta shi da ‘yan ta’adda

- Ministan tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya yi karin haske game da zargin da ake yi masa

- Pantami ya bayyana dalilin da yasa ake masa mugayen zarge zarge

- Jami’in ya dage cewa lallai sai an yi rajistar NIN

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami, ya ce zarge-zargen cewa yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi karya ce kawai.

Pantami ya fadawa jaridar Premium Times a wata hira ta musamman a ranar Juma’a, 16 ga watan Afrilu, cewa mutanen da ke adawa da yadda gwamnati ke hada lambar NIN da lambobin wayoyi sune ke yada zargin.

KU KARANTA KUMA: An shiga firgici yayinda shahararren Faston Najeriya ya mutu a cikin coci

A karshe ministan Buhari Isa Pantami ya magantu, ya bayyana dalilin da yasa ake alakanta shi da ‘yan ta’adda
A karshe ministan Buhari Isa Pantami ya magantu, ya bayyana dalilin da yasa ake alakanta shi da ‘yan ta’adda Hoto: @MallamRetweet
Asali: Twitter

Ya ce:

“Ba na shakka game da wannan. Yana da alaƙa da Lambar Shaida ta yan ƙasa. Kun san abu daya? An fara wannan tsarin a shekarar 2011, ba ta ci nasara ba. Me ya sa? An yake ta.''

Ya yi ikirarin cewa wasu tawaga sun dauki aniyar dakatar da manufar yin rajistar shaidar zama dan kasa ga dukkan ‘yan Najeriya da kuma wadanda ke zaune a kasar.

Ministan ya ce:

"A 2015, ya fito, bai yi nasara ba. A cikin 2018 akwai lokacin da aka yi ganawa tsakanin gwamnati da kamfanonin sadarwar wayoyin hannu. Kuma a zahiri an sanar da cewa ta hanyar yarjejeniya da gwamnati, wa'adin ya kasance watan Janairun 2018. Yana nan kan yanar gizo, zan nuna maku idan kuna so. Zuwa Janairu 2018, ba a aiwatar da shi ba, saboda akwai masu adawa da shi. Akwai tawaga!"

Pantami ya bayyana cewa rajistar ta NIN ba ta ‘yan Najeriya bane kadai.

Ya ce:

“Yanzu sun fara zuwa da labarin cewa mutane na zuwa daga kasashe makwabta don yin rijista.

“Abin da suka kasa fahimta shi ne cewa Lambar NIN kasa ba ta yan Najeriya kadai ba ce; kowa a Najeriya zai iya samunta."

Ministan ya bayyana cewa ba zai bar hare-haren da aka kai masa su dauke hankalinsa daga aikinsa ba.

KU KARANTA KUMA: Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan

Wasu ‘yan Najeriya sun yi kira ga Pantami da ya sauka daga mukaminsa bayan rahotanni sun yi zargin cewa wa’azin addinin Islama da yake yi a sassan arewacin kasar tsakanin farkon da tsakiyar shekarun 2000 ya kasance tsautsaura.

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rijistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.

Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin Tuwita.

Ministan ya ce za'a cigaba da rijistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel