Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan

Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan

- Bayan dawowarsa daga Landan inda ya je ganin likita, Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya cewa su yi tsammanin ci gaba daga gwamnatin sa

- Sai dai kuma Buhari bai bayyana ta wani bangare za a samu ci gaban ba

- A ranar Alhamis, 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar ya dawo gida Najeriya bayan shafe makonni biyu a kasar Ingila

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya cewa su yi tsammanin ci gaba daga gwamnatin sa bayan ya dawo daga jinyar da ya tafi yi a Landan, kasar Ingila.

Shugaban na Najeriya, mai shekaru 78, ya zanta da manema labarai lokacin da ya iso kasar ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a ranar Alhamis, 15 ga watan Afrilu da rana.

KU KARANTA KUMA: Malaman addinin Kirista sun yi bude bakin Ramadana da yan uwa Musulmi

Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan
Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

"Ci gaba," Buhari ya ce lokacin da aka tambaye shi abin da ya kamata 'yan Najeriya su tsammata daga gwamnatinsa. Sai dai kuma bai fayyace ko a wani bangare ba, Channels TV ta ruwaito.

Hutun da Buhari ya yi na mako biyu don ganin likita a Landan ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar. Masu sukar lamarin kuma mambobin babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyana damuwar su kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ke yi zuwa Ingila.

"Babban abin damuwa ne cewa a karkashin Shugaba Buhari, hatta asibitin da ake kula da shi a halin yanzu, ya zama abin da ba za ta iya samar da sauki ba a gare shi," in ji PDP a cikin wata sanarwa da ta kuma zargi gwamnatin Buhari da barnatar da kudin masu biyan haraji.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi babban rashi yayinda manyan jiga-jiganta 2 suka koma PDP tare da Magoya baya 1,000

A baya mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban tashar jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja daga birnin Landan bayan makonni biyu inda yaje ganin Likita.

Buhari ya dira Abuja ne misalin karfe 5 na yammacin Alhamis, 15 ga Afrilu 2021.

Mun kawo muku rahoton Jaridar Punch na ruwaito cewa komai ya kankama don dawowar shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel