Yanzu-yanzu: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi

Yanzu-yanzu: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi

- Bayan watanni da sanya takunkumi kan rijistan layukan waya, ministan sadarwa ya dage

- Pantami ya ce daga yanzu wajibi ne mutum ya gabatar da NIN kafin ayi masa rijista

- A cewarsa, Buhari ya jinjinawa ma'aikatar bisa namijin kokarin da sukayi

Gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rijistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.

Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin Tuwita.

Ministan ya ce za'a cigaba da rijistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.

Pantami ya ce an yanke shawaran cigaba da rijistan sabbin layuka ne bayan amincewar shugaba Buhari da sabon tsarin rijistan layuka da ma'aikatarsa ta samar.

"An kammala gyara-gyare kan tsarin bisa ga umurnin shugaban kasa inda aka wajabta amfanin da lambar NIN don rijistan sabon layi a jiya, 14 ga Afrilu, 2021," jawabin yace.

"Dr Pantami ya gabatar da tsarin ga shugaba Muhammadu Buhari...kuma (Buhari) ya jinjinawa ministan bisa kokarinsa wajen kawo cigaba sashen tattalin arzikin zamani da kuma atisayen hada layukan waya da NIN."

"Za'a fara aiwatar da sabon tsarin ranar Litnin, 19 ga Afrilu 2021. Hakazalika za'a cigaba da bada sabbin layuka da kuma sauran abubuwan da aka dakatar a ranar.

"Bugu da kari, Ministan ya umurci NCC da NIMC su tabbatar da cewa maus rijistan layukan da jama'a sun bi tsarin sau da kafa."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan

Yanzu-yanzu: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi
Yanzu-yanzu: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi
Asali: Original

KU KARANTA: Ina kan baka na, sai da gwamnatin tarayya ta buga N60bn don raba mana: Obaseki

A bangare guda, Ministan sadarwa na ƙasar nan, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargaɗi yan Najeriya waɗanda har yanzun ba su haɗa layukan wayar su da NIN ba da suyi gaggawar yi.

Ministan ya ce babu gudu ba ja da baya, dan haka kowa ya gaggauta haɗa nashi tun kafin lokaci yayi.

Isa Pantami ya faɗi haka ne a wasu zafafan sakonni da ya aike a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita ya yin da yake martani kan zargin da wasu jaridu ke masa da hannu a Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel