An shiga firgici yayinda shahararren Faston Najeriya ya mutu a cikin coci

An shiga firgici yayinda shahararren Faston Najeriya ya mutu a cikin coci

- Mutuwar Emeka Evans Unaegbu ya ba mazauna yankin Nyanya-Jikwoyi a Abuja mamaki

- Rundunar ‘yan sandan Abuja ta shawarci mazauna yankin da kar su yi saurin yanke hukunci game da mutuwar fasto din

- A yanzu, ‘yan sanda ba su zargin kowa game da lamarin

An shiga fargaba a yankin Nyanya-Jikwoyi da ke Abuja lokacin da aka ga wani sanannen fasto a yankin, Emeka Evans Unaegbu matacce a cocinsa.

Wasu majiyoyi sun fadawa Sahara Reporters cewa malamin ya gudanar da tsayuwar dare kafin aka gano shi a safiyar Laraba, 14 ga Afrilu, a harabar cocin ba rai.

Daga baya aka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

An shiga firgici yayinda shahararren Faston Najeriya ya mutu a cikin coci
An shiga firgici yayinda shahararren Faston Najeriya ya mutu a cikin coci Hoto: Stella Okoro, @PoliceNG
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Hukumomin tsaro sun dakile yunƙurin fasa gidan yarin Edo

Wata majiya da ke da masaniya game da lamarin ta ce:

“Da kyar yake numfashi a lokacin da makwabta da wasu mambobin cocin suka gano shi kwance a cikin ginin. Ya mutu yayin da aka garzaya da shi zuwa asibiti.”

Mazauna yankin sun nuna kaduwa kan lamarin.

A cewar jaridar The Sun, majiyoyin ‘yan sanda sun yi nuni da cewa mai yiwuwa mamacin ya fado ne daga kan matakala a yayin da yake gudanar da addu’o’i kasancewar bai samu raunin da zai iya danganta lamarin da harbin bindiga ko makamai ba.

KU KARANTA KUMA: Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan

Jami'an tsaro sun fara bincike don gano gaskiyar lamari game da mutuwar faston.

A wani labarin, iyayen daliban kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake Afaka a jihar Kaduna, sun ce an bukaci su biya kudin fansar 'ya'yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su.

An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan 'ya'yansu, Vanguard ta wallafa.

Duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng