Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu

Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu

- Ministan wutar lantarki, Sale Mamman ya roƙi gafarar yan Najeriya sabida matsalar rashin wutar lantarki da yan Najeriya suka fuskanta kwanan nan

- Ministan ya dangata hakan da lalacewar tashoshin samar da wutar da kuma rabata, amma ya tabbatar da ma'aikatarsa na aiki tuƙuru wajen warware matsalar

- Mamman ya tabbatar ma yan Najeriya da cewa duk komai zai dawo dai-dai, zasu ga haske kamar yadda suka saba gani

Mininistan wutar lantarki, injiniya Sale Mamman ya nemi gafarar yan Najeriya bisa tsaikon wutar lantarki da aka fuskanta a faɗin ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari

A wani saƙo da ya fitar ranar Alhamis, Mamman yace yayi dana sanin irin matsanancin halin da rashin wutar ya haifar wa yan Najeriya.

Ministan yace matsalar ta farune daga tashoshin wutar lantarki waɗanda suke da alhakin raba wuyar ga yan Najeriya, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu
Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu Hoto: @powerminNigeria
Asali: Twitter

Mamman yace:

"Nayi matuƙar dana sanin ƙarancin wutar lantarki a faɗin ƙasar nan, da kuma wahalhaƙun da hakan ya haifar. Ina mai tabbatar ma yan uwana yan Najeriya cewa muna aiki tuƙuru wajen ganin komai yadawo yadda yake ko ma yawuce haka."

"An samu matsalar ne saboda lalacewar da wasu tashoshin wutar lantarkin waɗanda suke aikin raba wutar. Tashoshin da suka samu matsalar sun haɗa da: Sapele, Afam, Olonrunsogo, Omotosho, Ibom, Egbin, Alaoji da kuma Ihovbor."

KARANTA ANAN: Gwamnoni sun buƙace sake zama na musamman domin duba matsalar tsaron Ƙasar nan

Mamman ya tabbatarma yan Najeriya cewa ma'aikatar wutar tana aiki tuƙuru don ganin an gyara dukkan matsalolin da ake fuskantar tashoshin samar da wutar lantarki da kuma matsalar man gas da sauransu.

Ya kuma ƙara jaddada aniyar ma'aikatar wutar lantarki na dawo da wutar da ake samarwa a farkon wannan shekarar wacce takai 5,600MW.

A wani labarin kuma Wasu Yan bindiga sun kashe mutane huɗu a wani sabon hari da suka kai jihar Taraba

Wasu yan bindiga sun sake kai sabbin hare-hare a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Taraba, inda suka kashe mutum huɗu.

Yan bindigar sun kai hari kauyukan ne da daren Laraba, suka kashe mutum huɗu tare da jikkata wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel