Wasu Yan bindiga sun kashe mutane huɗu a wani sabon hari da suka kai jihar Taraba

Wasu Yan bindiga sun kashe mutane huɗu a wani sabon hari da suka kai jihar Taraba

- Wasu yan bindiga sun sake kai sabbin hare-hare a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Taraba, inda suka kashe mutum huɗu

- Yan bindigar sun kai hari kauyukan ne da daren Laraba, suka kashe mutum huɗu tare da jikkata wasu da dama

- Shugaban ƙaramar hukumar da kauyukan ke ƙarƙashinta ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce zasu ɗau mataki

Kwana biyu kacal da yan bindiga suka kashe wani mutumi a kauyen Ikyaior ƙaramar hukumar Wukari jihar Taraba. Wasu yan bindigar sun sake kashe mutane huɗu a wani hari na daban a ƙauyen ranar Laraba da daddare.

KARANTA ANAN: Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari

Wani mazaunin ƙauyen, Mr. Msuuve Aondoakaa, ya faɗawa wakilin Punch cewa yan bindiga kimanin 20 sun afkama kauyen Tor-Iorshagher ind suka kashe mutum ɗaya suka jikkata wasu da dama.

Aondoakaa wanda ya koka kan yawan kai hare-hare yankin, ya yi kira ga gwamnan jihar, Darius Ishaku, da ya magance musu matsalar tsaron da ta addabi yankin.

A wani harin kuma na daban da aka kai wani gari dake kusa, Rafinkada, Mrs. Joy Audu, wani.mazaunin garin ya bayyana cewa wasu yan bindiga sun kashe mutum uku, sun kuma harbi wasu da dama.

Shugaban ƙaramar hukumar, Mr. Daniel Adi, ya tabbatar da kai hare-haren guda biyu a wurare daban-daban.

Wasu Yan bindiga sun kashe mutane huɗu a wani sabon hari da suka kai jihar Taraba
Wasu Yan bindiga sun kashe mutane huɗu a wani sabon hari da suka kai jihar Taraba Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Adi, ya ce ya ziyarci kauyukan da abun ya faru kuma ya bada umarnin rufe waɗanda suka mutu.

KARANTA ANAN: Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya

Shugaban ya ce ya kuma kira taron tsaro domin tattaunawa kan yadda za'a shawo kan waɗannan hare-haren a yankin.

Da aka tambayeshi kan waɗanda suka mutu yace:

"Eh hakane, tabbas mutum daya ya mutu kuma ɗaya ya samu rauni a ƙauyen Tor-Iorshagher. Haka kuma mutane uku sun mutu ya yinda biyu suka samu rauni daga harbin bindiga."

"Yanzun nan na dawo daga kauyukan da lamarin ya faru. Dukkan yankunan biyu sun kwantar da hankalinsu kuma zamu yi taro dasu kan yadda zamu shawo kan faruwar irin haka nan gaba."

A wani labarin kuma Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya

Sananniyar jaruma kuma ma'aikaciyar gidan talabishin ta rigami gidan gaskiya bayan kwanciya a Asibiti na ɗan ƙanƙanin lokaci.

Ɗan uwan jarumar kuma ƙaninn ta ne ya tabbatar da rasuwarta a wata zantawa da aka yi dashi ta wayar salula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel