Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari

Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari

- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzun gwamnatinsa bata manta da ragowar yan matan makarantar Chibok dake hannun mayaƙan Boko Haram ba

- Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin babban mai taimaka masa kan harkokin yaɗa Labarai, Garba Shehu

- Ya kuma roƙi yan Najeriya da su cigaba da goyon bayan gwamnati da kuma yima sojoji addu'a don ganin sun sami nasara a dukkan yaƙin da suke yi

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ƙara tabbatar ma da iyaye da kuma yan ƙasa nagari cewa bata mance da yan matan makarantar Chibok dake hannun yan ta'adda ba.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Sun sheƙe wasu yan fashin teku 4 a jihar Akwa Ibom

Gwamnatin ta ce ɗaliban suna cikin zuciyar gwamnati kamar yadda suke a cikin zuciyoyin iyayensu.

Wannan na ƙunshe a cikin wani saƙo da Malam Garba Shehu, babban mai taimaka ma shugaba Buhari ta harkar yaɗa labari, ya fitar a shafinsa na Tuwita.

Mayaƙan Boko Haram sun sace ɗalibai mata 276 a makarantar sakandiren mata ta gwamnati dake Chibok jihar Borno a ranar 14 ga watan Afrilu, 2014.

Yan ta'addan sun yi wannan aika-aika ne a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan.

Sai dai bayannan wannan, an samu satar ɗalibai da dama a ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasa Buhari.

Da Ɗuminsa: Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari
Da Ɗuminsa: Ban manta da ragowar Yan matan Chibok dake hannun Yan Boko Haram ba, Inji shugaba Buhari Hoto: @mobilepunch
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Bayan ta kafa tarihin fita da sakamako mafi kyau a jami'a, yar Nageriya ta samu tallafin zuwa Amurka

Amma Garba Shehu ya ƙara tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa gwamnati bata manta ba, kuma aikin ceto ragowar yan matan na nan ana cigaba da yinsa.

"Ƙoƙarin ganin an sako sauran ɗalibai matan dake hannun yan ta'addan Boko Haram ɗin na nan na cigaba yadda ya kamata." inji Shehu.

Na kusa da shugaban ƙasan ya roƙi iyayen da kuma yan Najeriya da su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya da kuma baiwa jami'an haɗin kai don ganin sun gudanar da aikin su cikin nasara.

Legit.ng Hausa ta tattauna da fitacciyar yar fafutukar nan ta BBOG, ƙungiyar rajin dawo da yan matan Chibok, Aisha Yusuf.

Tace: "Ya zuwa yanzun akwai ragowar ɗalibai mata guda 112 a hannun su, an saki 107. A duk shekara ranar 14 ga watan Afrilu gwamnati na fito da jawabinta daga nan kuma shikenan sai su watsar da lamarin."

"Iyayen yarannan ba jawabi suke buƙata ba kawai so suke suga yayan su na tare da su, yanzun shakara bakwai kenan kan mu farga sai kaji ance shekaru 20 sun wuce"

A wani labarin kuma Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya

Sananniyar jaruma kuma ma'aikaciyar gidan talabishin ta rigami gidan gaskiya bayan kwanciya a Asibiti na ɗan ƙanƙanin lokaci.

Ɗan uwan jarumar kuma ƙaninn ta ne ya tabbatar da rasuwarta a wata zantawa da aka yi dashi ta wayar salula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262