Gwamnoni sun buƙace sake zama na musamman domin duba matsalar tsaron Ƙasar nan

Gwamnoni sun buƙace sake zama na musamman domin duba matsalar tsaron Ƙasar nan

- Gwamnonin ƙasar nan sun buƙaci a sake zama na musamman domin duba matsalar tsaron ƙasar nan domin kullum abubuwa ƙara taɓarɓarewa suke

- Gwamnonin sun faɗi haka ne jim kaɗan bayan fitowa daga taron ƙungiyar su a jiya Laraba, taron da ya ɗau tsawon lokaci ana yinsa

- Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban ƙungiyar Gwamnonin (NGF) ya ce ya zama wajibi a sake duba fannin tsaron ƙasar nan

Ƙungiyar gwamnonin ƙasar nan (NGF) ta buƙace a sake zama na musamman don duba matsalar tsaron ƙasar nan kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Gwamnonin sun yi wannan kiran ne ranar Laraba a wani taro wanda shugaban ƙungiyar NGF ɗin kuma gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya jagoranta a Abuja.

KARANTA ANAN: Bayan ta kafa tarihin fita da sakamako mafi kyau a jami'a, yar Nageriya ta samu tallafin zuwa Amurka

Ya yin da yake bayyana ma manema labarai bayan taron wanda yakai har tsakiyar dare, gwamna Fayemi yace sake duba matsalar tsaro ya zama wajibi.

Gwamnan ya ce "Zaman sake duba matsalolin tsaro ya zama wajibi a yanzun, sannan a saka mahukuntan ƙasar nan waɗanda suka haɗa da yan siyasa da hukumomin tsaro domin a gano hanyoyin warware matsalar data ƙi ci taki cinyewa."

Ya ƙara da cewa gwamnonin ƙasar nan sun damu matuƙa biyo bayan hare-haren da aka kai kan jami'an gyaran hali da kuma yan sanda a jihar Imo.

Gwamnoni sun buƙace sake zama na Musamman domin duba matsalar tsaron Ƙasar nan
Gwamnoni sun buƙace sake zama na Musamman domin duba matsalar tsaron Ƙasar nan Hoto: @NGFsecritariat
Asali: Twitter

Da kuma kisan da akai wa wasu sojoji a jihar Benuwai da sauran hare-hare da ake cigaba da kaiwa a wasu sassan ƙasar nan.

An dai samu ƙarin matsalar tsaro a Najeriya inda yan bindiga da yan ta'adda suka ƙara yawan kai hare-hare a arewacin ƙasar, a kudanci kuma ana kaima jami'an tsaro hari.

KARANTA ANAN: Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya

Aƙalla wuraren yan sanda uku aka kaima hari a jihar Imo cikin watan Afrilu, wanda suka haɗa da hedkwatar yan sandan ta jiha.

Sannan kuma aƙalla fursunoni 1,800 suka kuɓuta daga gidan gyaran hali a Owerri biyo bayan harin da yan bindiga suka kai gidan.

Hakanan kuma an samu rikice-rikice da yawa a jihohin kudancin ƙasar nan da suka haɗa da; Oyo, Ogun da kuma jihar Rivers.

Yan bindiga sun kai hari a ƙauyuka da yawa a wasu jihohin Arewa da suka haɗa da; Kaduna, Zamfara, Benuwai da sauran su.

A wani labarin kuma Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

Gwamnatin Najeriya ta ƙirƙiro da hanyoyi da dama domin rage raɗaɗin da annobar COVID19 ta jefa ɗai-ɗaikun yan Najeriya da kuma yan kasuwa.

Ɗaya daga cikin abun da ta ƙirƙiro shine shirin bada rance daga CBN wanda akaima laƙabi da TCF kuma bankin NIRSAL MICROFINACE ke tafiyar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262