Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo da Ondo a mulkin soja, Usman, ya mutu

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo da Ondo a mulkin soja, Usman, ya mutu

- Allah ya yi wa tsohon gwamna jihar Oyo da Ondo na mulkin soja, Kanal Ahmed Usman, rasuwa

- Usman ya rasu ne da misalin karfe 3.00am na ranar Laraba a Jos, babban birnin jihar Filato, yayin wani rashin lafiya

- Ya mulki jihar Ondo daga watan Agusta 1994 zuwa Agusta 1996, sannan ya mulki Oyo daga watan Agusta 1996 zuwa Agusta 1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.

Tsohon gwamna jihar Oyo na mulkin soja, Kanal Ahmed Usman, ya amsa kiran mahaliccinsa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Usman ya rasu ne da misalin karfe 3.00am na ranar Laraba a Jos, babban birnin jihar Filato, yayin wani rashin lafiya.

An tattaro cewa an tafi da gawarsa zuwa kauyensa, Okura-Lafia, jihar Kogi don binne shi kamar yadda addinin musulinci ya tanadar.

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo da Ondo a mulkin soja, Usman, ya mutu
Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo da Ondo a mulkin soja, Usman, ya mutu Hoto: The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Mutane da yawa sun mutu a rikicin kabilanci a kan iyaka a Gombe, Adamawa

Jaridar Tribune ta kuma tabbatar da mutuwar Usman daga danginsa.

Daya daga cikin yan uwan marigayi tsohon gwamnan na soja ya ce:

“Oga ya tafi. Mun rasa shi a safiyar yau.”

Usman ya kasance gwamnan jihar Ondo na mulkin soja daga watan Agusta 1994 zuwa Agusta 1996.

Ya yi gwamnan Oyo daga watan Agusta 1996 zuwa Agusta 1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.

A matsayinsa na shugaban MILADS na jihohin Odu’a, ya yi gwagwarmaya da mutanen da suka sayi kadarorin kamfanonin Odu’a, wanda aka dawo da wasun su.

A gefe guda, a wani rahoto da Vanguard ta fitar ya nuna cewa a kalla gawawwaki 15 ne aka gano a ranar Talata, 13 ga Afrilu, a yankin Miles Five da ke wajen Calabar.

A cewar rahoton, gawawwakin da suka hada maza da mata an jefar da su a cikin wani kwari da ke kan babbar hanyar mota biyu da gwamnan Cross River, Ben Ayade yake ginawa.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar

Har yanzu ba a san waɗanda suka aikata munanan ta’asar ba yayin da ba a san dalilinsu na aikata mummunan aikin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel