Mutane da yawa sun mutu a rikicin kabilanci a kan iyaka a Gombe, Adamawa

Mutane da yawa sun mutu a rikicin kabilanci a kan iyaka a Gombe, Adamawa

- Rikicin kabilanci a Najeriya ya yi kamari musamman a yankunan da ke kan iyaka

- A yanzu haka garuruwa a Gombe da Adamawa suna cikin rikici wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu mutane

- Mahukunta sun ayyana dokar hana fita a yankin yayin da ake kokarin dawo da zaman lafiya

An bayar da rahoton kashe mutum biyar a wani rikicin kabilanci tsakanin garuruwan da ke kan iyaka na Nyuwar / Jessu a jihar Gombe wanda ya kunshi mutanen Waja da Lunguda a jihar Adamawa a ranar Talata, 13 ga Afrilu.

Shaidu sun ce rikicin ya samo asali ne sakamakon rashin fahimta tsakanin mafarauta daga Jessu da Fulani daga Lunguda a Adamawa wadanda a koda yaushe suke shakkar kansu.

Shaidu sun ce wata kungiya daga Jessu ta je daji farauta a lokacin da yaran Fulanin suka gansu suka ja hankalin jama’a.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar

Mutane da yawa sun mutu a rikicin kabilanci a kan iyaka a Gombe, Adamawa
Mutane da yawa sun mutu a rikicin kabilanci a kan iyaka a Gombe, Adamawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wani ganau ya fadawa jaridar The Nation:

“Abin da muka ji shi ne lokacin da yaran Fulanin suka ga mafarautan sai suka yi karar cewa mafarautan suna kai musu hari kuma suka sanar da mahaifinsu.

"Fulanin sun zo suka fara harbi, har zuwa yanzu da nake magana da kai suna ci gaba da fada da kona gidaje."

Kwamishinan 'yan sanda, Ishola Babaita, ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa inda lamarin ya faru kuma ba zai iya cewa komai ba tukuna.

An ce Gwamna Inuwa Yahaya da sauran manyan ma'aikatan gwamnati suna kan hanyarsu ta zuwa inda lamarin ya faru.

Don magance tashin hankali, gwamnatin jihar Gombe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankunan da lamarin ya shafa nan take.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa akalla mutane 10 aka kashe a rikicin.

A cewar rahoton, makwabtan da ke raba matsugunan kan iyaka sun yi ta fama da rikici tsawon shekaru.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 6 da yan Najeriya basa so game da gwamnatin Shugaba Buhari

Gidan Talabijin na AIT ya bayar da rahoto cewa wadanda suka rasa rayukansu a rikicin sun kusan 15.

Rahoton ya yi nuni da cewa yankunan da abin ya shafa sun kasance wuraren da rikici ya barke tsakanin kabilun Waja da Lunguda, kan filaye.

A wani labari, adadin mutanen da suka suka mutu sakamakon harin da Boko Haram ta kai garin Kwapree a karamar hukumar Hong na jihar Adamawa ya kai 10.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu mazauna garin a ranar Litinin suka ce yan ta'addan Boko Haram sun kira su suna neman a biya Naira Miliyan 30 kafin su sako mutum 30 d suka sace a yayin harin da suka kai garin, rahoton The Punch.

Shugaban karamar hukumar, James Pukama, a ranar Litinin yace yayin ziyarar da kakakin majalisar jihar Adamawa ya kai, adadin wadanda suka mutu ya karu daga bakwai zuwa 10 bayan gano wasu gawarwaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel