Tashin hankali: An gano gawawwaki ba tare da kai ba a karkashin gada a Cross River

Tashin hankali: An gano gawawwaki ba tare da kai ba a karkashin gada a Cross River

- Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kashe wasu bayin Allah a jihar Cross River

- Kodayake ba a san ainihin lokacin da mummunan lamarin ya faru ba, wani ganau ya ce an gano gawawwakin wadanda abun ya cika da su a ranar Talata, 13 ga Afrilu

- Zuwa yanzu hukumar yan sandan jihar bata ce komai ba a kan lamarin

Wani rahoto da Vanguard ta fitar ya nuna cewa a kalla gawawwaki 15 ne aka gano a ranar Talata, 13 ga Afrilu, a yankin Miles Five da ke wajen Calabar.

A cewar rahoton, gawawwakin da suka hada maza da mata an jefar da su a cikin wani kwari da ke kan babbar hanyar mota biyu da gwamnan Cross River, Ben Ayade yake ginawa.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar

Tashin hankali: An gano gawawwaki ba tare da kai ba a karkashin gada a Cross River
Tashin hankali: An gano gawawwaki ba tare da kai ba a karkashin gada a Cross River Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Har yanzu ba a san waɗanda suka aikata munanan ta’asar ba yayin da ba a san dalilinsu na aikata mummunan aikin ba.

A cewar wani rahoto na jaridar The Punch, shaidu, wadanda suka kasance a wurin, sun ce manoma sun fara gano gawawwakin ne da sanyin safiya kafin daga baya jama’a suka taru a wurin.

Wani direban haya, Alex, wanda ke wurin, ya ruwaito cewa ta yiwu wasu mutane ne suka kawo gawawwakin a cikin abin hawa sannan suka jefar da su a daren ranar Litinin, Afrilu 12.

An ruwaito shi yana cewa watakila an kashe mutanen ne a Calabar kuma aka kai su yankin da babu kowa.

"Ina mamakin dalilin da ya sa 'yan sanda da jami'an tsaro da suka sanya shingayen kan wannan hanyar ba za su iya tare su ba saboda warin da ke fitowa daga irin wadannan gawawwakin na iya zama mai karfi."

Wani ganau a wurin, Nsikak Etim, ya ce ba zai iya kirga yawan gawawwakin da aka jefa a can ba saboda mawuyacin hali.

An tattaro cewa wurin ba shi da nisa sosai da shingen binciken 'yan sanda da jami'an tsaro a kan babbar hanyar Calabar-Odukpani.

KU KARANTA KUMA: Fasto Adeboye ya bayyana gaskiyar lamari game da Gwamna El-Rufai

An ce an kwashe gawawwakin a yammacin ranar karkashin kulawar 'yan sanda.

A wani labarin, baya ga makudan kudaden da ake biya a matsayin fansa ga masu satar mutane daga iyalan mutanen da aka sace, a yanzu haka ‘yan bindigan sun nemi a basu buhunan shinkafa da kayan miya a matsayin wani bangare na fansa.

Al’umomin karkara da ke yankunan Kuje, Kwali, Gwagwalada da kuma Abaji sun shaida ci gaba da kai hare-hare, inda aka sace sama da mutane 30 a cikin watanni uku da suka gabata kuma suka karbi kudin fansa na miliyoyin nairori.

Amma kwanan nan, yayin sace wasu mazauna yankin Kiyi da Anguwar Hausawa, masu garkuwar sun gaya wa iyalan wadanda suka yi garkuwar da su kawo buhunan shinkafa, taliya, supageti da kuma katan din maggi tare da kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel