Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar

Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar

- Gobara ta halaka dalibai 20 a makarantar firamare da ke unguwar Pays Bas a birnin Yamai, Jamhuriyar Nijar

- Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Talata, 13 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:00 na yamma

- Zuwa yanzu dai ba a san ainahin abunda ya haddasa gobarar ba

An shiga halin fargaba da makoki a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar bayan gobara ta halaka 'yaran makaranta fiye da ashirin da yammacin ranar Talata, 13 ga watan Afrilu.

An tattaro cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 4:00 na yamma a makarantar firamare da ke unguwar Pays Bas a birnin Yamai, inda azuzuwa 28 da aka yi su da zana suka kone kurmus tare da halaka dalibai kananan yara akalla 20.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 6 da yan Najeriya basa so game da gwamnatin Shugaba Buhari

Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar
Abun bakin ciki: Gobara ta lakume daliban makaranta 20 a Nijar Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa gobarar ta fara tashi ne daga kofar shiga makarantar, mai dalibai akalla 800.

Sai dai kuma har yanzu ba a san abunda ya haddasa gobarar ba.

A halin yanzu hukumar kashe gobara ta kasar ta ce azuzuwan suna manne da juna lamarin da ya sa gobarar ta munana, yaran kuma suka makale babu ta inda za su fita.

Shugaban hukumar kwana-kwana na birnin Yamai ya ce jami'ansa sun isa makarantar cikin gaggawa, an kuma yi nasarar kashe wutar.

Sai dai ya ce an kafa azuzuwan ne a kusa da rariya, kuma iska ta yi ta kadawa wadda ita ma ta kara rura wutar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato jami'in kungiyar malamai Mounkaila Halidou na cewa: "Rashin kofar fitar gaggawa ya sa dalibai da dama sun makale sannan ya tilasta wa wasu haura katanga. Wadanda suka mutu yawanci kananan yara ne da ke matakin raino."

Firai ministan Ouhoumoudou Mahamadou da ministan ilimin kananan makarantu da gwamnan birnin Yamai sun kai ziyara makarantar, tare da yin jaje da ta'aziyya ga iyayen yaran da suka rasu.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin Gwamna ya tsere da motocin Gwamnati 4 watanni 2 da barin kujerar mulki

A wani labarin kuma, wata Baiwar Allah mai suna Lubna Ali ta jawo abin magana bayan ta bayyana irin tsananin soyayyar da ta ke yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Lubna Ali a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa a dalilin kaunar da ta ke yi wa Madugun Kwankwasiyya, ta ki amsa tayin aure da wani ya yi mata.

Wannan budurwa ta yi magana da jaridar Sahelian Times inda ta sake tabbatar da cewa ba za ta taba auren duk saurayin da bai ganin mutuncin gwarzonta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng