El-Rufai ya bayyana dalilansa na rage ma'aikata a Kaduna

El-Rufai ya bayyana dalilansa na rage ma'aikata a Kaduna

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi fashin bakin kan dalilin rage ma'aikata a jiharsa

- El-Rufai ya ce kudaden da gwamnatin jihar ke kashewa wurin biyan albashi ya yi wa jihar yawa, bayan albashin ba a samun kudin yin wasu ayyukan

- Gwamnan ya ce ma'aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa ne ke cinye fiye da kashi 90 cikin 100 na kudin jihar

- Rashin adalci ne mutanen da ba su kai 100,000 ba su rika cinye fiye da kashi 90 na cikin kudin jihar yayin da sauran wadanda ba ma'aikatan gwamnati ba su morar komai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya yi bayanin abin da yasa gwamnatinsa ke rage ma'aikata a jihar.

Ya ce hakan ya zama dole ne domin jihar ba ta da kudin da za ta cigaba da yi wa mutane ayyuka gami da yawan albashin da ta ke biya a lokacin da kudaden da gwamnatin tarayya ke bawa jihohi duk wata (FAAC) bai karu ba.

El-Rufai ya bayyana dalilansa na rage ma'aikata a Kaduna
El-Rufai ya bayyana dalilansa na rage ma'aikata a Kaduna. Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue

Gwamnan ya ce kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya, FAAC, tun tsakiya shekarar 2020 kamar sauran jihohi, da kyar ya ke isa a biya albashi ballantana a yi wasu ayyukan.

Ya ce wannan aikin rage ma'aikatan zai shafi masu rike da mukaman siyasa inda ya ce an yi hakan ne domin rage kudaden da ake kashewa.

El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin ta bakin mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye.

Ya ce: "A Nuwamban 2020, abin da ya rage wa gwamnatin Kaduna bayan biyan albashi shine N162.9m. A wannan watan jihar ta samu N4.83bn daga FAAC sannan ta biya albashi da N4.66bn."

Bayanin ya nuna watannin da suka biyo baya kusan lamarin bata canja zani ba wato dai da an biya albashi babu wani kudin da jihohin za ta yi wasu ayyukan da su.

KU KARANTA: Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

Gwamnan ya ce bai kamata jiha da ke da ma'aikatan gwamnati kasa da 100,000 su rika lakume fiye da kashi 90 cikin 100 na kudaden jihar, su bar wa sauran da ba ma'aikatan gwamnati bane ko masu rike da mukaman siyasa kaso kalilan.

"Wannan rashin adalci ne 'yan tsiraru su rika cinye kaso mafi tsoka na kudin jihar.

"Ma'aikatan gwamnati na da muhimmanci don haka ya kamata a kayyade dai-dai adadin da ake bukata."

Asali: Legit.ng

Online view pixel