Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue

Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue

- A yau Litinin 12 ga watan Afrilu ne aka yi jana'izar sojoji 12 da yan bindiga suka kashe a, Konshisha jihar Benue

- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya hallarci jana'izar inda ya yi alkawarin ganin an samar da zaman lafiya a Konshisha

- Malaman addinin musulunci da kirista na sojoji ne suka jagoranci jana'izar inda suka ce jaruman sojojin sun rasu ne wurin kokarin samar da zaman lafiya

An kawo gawarwakin sojoji 12 da wasu yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Konshisha a Benue zuwa makabartar sojoji da ke Wurukum a Makurdi babban birnin jihar don musu jana'iza.

Daily Trust ta ruwaito cewa gawarwarkin jami'in soja daya da dakarun sojoji 11 suna kwance a makabartar a yanzu.

KU KARANTA: Hotunan gidajen da 'yan bindiga suka kona a Ondo saboda 'yan garin sun bawa jami'an tsaro bayannan sirri

Manyan jami'an sojoji sun hallara wurin, suna jirar a fara yin jana'izar na sojojin.

Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue
Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue. Hoto: TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun sace mata 30 bayan kashe mutum biyar a Adamawa

A baya, rundunar sojojin ta sanar da cewa sojojin 11 da jami'in daya da aka kashe suna aikin samar da zaman lafiya ne tsakanin mutanen Bonta a Konshisha da Ukpute-Ainu a karamar hukumar Okay da ke rikici kan filaye.

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom shima ya samu hallartar wurin jana'izar sojojin.

Ortom ya nuna bakin cikinsa bisa kashe sojojin ya kuma ce zai hada kai da jami'an tsaro domin dawo da zaman lafiya a Konshisha.

Malaman addini da suka jagoranci addu'o'i wurin jana'izan, Major Ibrahim Mavisky da Imam Captain A.A. Bashir duk sun ce haka rayuwa ta ke, akwai lokacin haihuwa da mutuwa.

Sun kara da cewa jaruman da suka rasu masu kokarin kawo zaman lafiya ne amma abin takaici suka rasa rayyukansu wurin aikata hakan.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel