Badaƙalar Kuɗin Makamai: Daga ƙarshe, shugaban Sojoji COAS ya bayyana a gaban yan majalisa
- Yanzun haka shugaban rundunar sojojin ƙasar nan ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi da majalisa ta kafa don bincikar yadda aka yi da kuɗin makamai
- A kwanakin baya dai kwamitin ya aike da katin gayyata ga Shugaban sojin da kuma gwamnan babban bankin Najeriya amma basu sami zuwa ba
- Kwamitin ya aike da katin gayyata ga mutanen biyu ne dan suzo amsa tambayoyi kan yadda aka yi da kuɗin makamai, idan an siya ina aka kaisu
Rahotanni daga jaridar Punch sun bayyana cewa shugaban sojojin ƙasar nan, Ibrahim Attahiru, (CAOS) ya bayyana a gaban kwamitin majalisa don amsa tambayoyi.
KARANTA ANAN: Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani
Majalisar ta kafa kwamitin ne domin bincikar yanda aka siya, aka yi amfani da makamai da harsasai da sauran kayan yaƙi a rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro.
Kwamitin ya gayyaci shugaban sojojin aƙalla sau biyu domin yazo ya amsa tambayoyi kan yadda aka siya makaman da kuma yadda aka yi amfani da su.
Hakanan kwamitin ya gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya, Gowin Emefiele, da ya bayyana a gabansu domin amsa tambayoyin kan kuɗin makamai da aka ware.
KARANTA ANAN: Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa
Sai dai a ranar Jumu'a, kwamitin ya ɗage zaman har zuwa ranar Litinin bayan dogon jiran waɗanda aka gayyata ɗin ba su zo ba.
A kwanakin baya, ranar 22 ga watan Maris 2021, kwamitin ya gayyaci manyan mutanen biyu, gwamnan CBN da kuma COAS.
Amma saboda rashin amsa gayyayar kwamitin da suka yi, yan majlisun dake cikin kwamitin sun sake basu wa'adin su bayyana kafin 7 ga watan Afrilu.
A wani.labari kuma EFCC ta bayyana dalilin da yasa take Amfani da Otal ɗin da aka ƙwace a hannun Dasuƙi
Hukumar dake yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta bayyana dalilin da yasa take amfani da Otal ɗin da aka kwace a hannun Sambo Dasuƙi.
Shugaban EFCC reshen jihar Kaduna ya ce jami'an su na amfani da wurin ne na ɗan wani lokaci musamman waɗanda aka canza ma wurin aiki zuwa Kaduna.
Asali: Legit.ng