Kuɗin Makamai: EFCC ta bayyana dalilin da yasa take Amfani da Otal ɗin da aka ƙwace a hannun Dasuƙi

Kuɗin Makamai: EFCC ta bayyana dalilin da yasa take Amfani da Otal ɗin da aka ƙwace a hannun Dasuƙi

- Hukumar dake yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta bayyana dalilin da yasa take amfani da Otal ɗin da aka kwace a hannun Sambo Dasuƙi.

- Shugaban EFCC reshen jihar Kaduna ya ce jami'an su na amfani da wurin ne na ɗan wani lokaci musamman waɗanda aka canza ma wurin aiki zuwa Kaduna

- Sai dai wata ƙungiyar matasa dake Badarawa ta yi zargin cewa kayayyakin amfani na cikin Otal ɗin sun yi ɓatan dabo

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana dalilin da yasa take amfani da Otal ɗin da ta ƙwace daga hannun tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuƙi.

KARANTA ANAN: Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Rahotanni sun tabbatar da cewa EFFC ta ƙwace Halal Fountain Hotel (Annex) dake lamba 29A, hanyar Rabah, jihar Kaduna daga hannun Sambo Dasuƙi.

Kwanakin baya dai, jaridar Dailytrust ta ruwaito yadda Otal ɗin da ake bincike akansa kan zargin batar dala biliyan $2.1bn kuɗin makamai wanda Sambo Dasuki ke da hannu a ciki, ya zama wurin hutun wasu daga cikin jami'an hukumar EFCC.

Shugaban hukumar EFCC reshen jihar Kaduna, Sanusi Abdullahi ya tabbatar da wasu jami'an su na amfani d Otal ɗin.

Ya ce jami'an da aka canza ma wajen aiki zuwa Kaduna na amfani da wurin a matsayin masaukin su na wani lokaci.

Sai-dai wata ƙungiyar matasan Badarawa sun bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin Otal ɗin da suka haɗa da talabishin ɗin dakunan Otal ɗin sun yi ɓatan dabo.

Amma Abdullahi ya ce ba gasƙiya bane abinda matasan suka faɗa cewa wasu kayayyakin wajen sun ɓace.

Ya kuma ƙara da cewa EFCC ta yi namijin ƙoƙari wajen tabbatar kayan amfani Otal ɗin basu lalace ba.

KARANTA ANAN: Ba zamu zuba ido muna Kallo ana kashe mana Mutane a Kudu ba, Sanata Babba kaita ya yi kakkausan Gargaɗi

Shugaban hukumar na jihar Kaduna ya ɗakko hotunan kayan cikin Otal ɗin don tabbatar da maganar sa cewa hukumar na amfani da wurin ne na ɗan wani lokaci.

Sai dai duk da haka wakilin jaridar Dailytrust bai tabbatar da ko kayayyakin cikin Otal ɗin nanan yadɗa suke ba, saboda sun hana shiga ɗakunan cikin Otal ɗin.

Sannan kuma kofar shiga Otal ɗin abuɗe take kuma wakilin ana hangen abuɓuwa hawa a harabar cikin sa.

Amma wani mutumi da ya fito daga cikin Otal ɗin ya bayyana cewa wurin na ƙarƙashin bincike saboda haka ba kowa ke amfani da shi ba.

Muttumin ya ce: "Jami'an EFCC da suka fito daga wajen ɗaukar horo ne kaɗai ke amfani da wajen. Kuma sunce suna amfani da shi ne na ɗan wani lokaci kafin su sami wurin zama na din-din din."

A wani labarin kuma Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadana daga ranar Litinin

Sarkin ya bada wannan umarnin ne ta hanyar shugaban kwamitin bada shawara kan al'amuran addinin musulci na fadarsa dake Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: