Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani

Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani

- Babban Bankin Najeria CBN ya ce shi baisan da zancen buga sabbin kuɗi na kimanin biliyan N60bn da ake cewa gwamnati ta yi a watan Maris ba

- A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa gwamnati bata da kuɗi, saida aka buga sabbi na 60 biliyan don rabawa a matakan gwamnati a watan Maris

- Hakanan itama ma'aikatar kuɗi ta ƙasar nan tace sam bata da wannan labarin sai dai a tuntuɓi CBN

Babban bankin Najeriya CBN ya ƙaryata cewa Najeriya ta buga sabbin kuɗi na kimanin 60 biliyon a watan da ya gabata saboda matsalar kuɗin da ta shiga.

KARANTA ANAN: Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa

Wannan ya biyo bayan jawabin da gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya yi inda yace Najeriya ta ƙera sabbin kuɗi 60 biliyan don rabawa a tsakanin matakan gwamnati uku.

Obaseki ya bayyana haka ne ranar Alhamis inda yace Najeriya na cikin rashin kuɗi Kamar yaɗda Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma kara cewa saida aka ƙera sabbin kuɗi na kimanin biliyan N60bn a watan Maris ɗin da ya gabata.

Gwamnan ya kuma nuna rashin jin daɗinsa a kan yawan rance da gwamnati ke yi, yana mai cewa ba dai-dai bane a cigaba da ciyo bashi ba tare da yin tsarin yadda za'a biya kuɗin ba.

Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani
Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun CBN, Osita Nwanisobi, da ya yi jawabi kan maganar gwamnan, ya ce shikam bashi da labarin an buga sabbin kuɗi har 60 biliyan.

KARANTA ANAN: Rikicin Hijabi: Madalla! An Buɗe makarantun da rikicin Hijabi ya shafa a Jihar Kwara

"Ni bani da labarin an buga sabbin kuɗi a watan da ya gabata," Nwanisobi ya faɗawa ɗaya daga cikin wakilan Punch.

Hakanan kuma, da aka tuntuɓi ma'aikatar kuɗin ƙasar nan kan buga sabbin kuɗi na 60 biliyan a watan Maris, ma'aikatar tace wannan tambayar gwamnan da ya faɗi haka shi za'a tambaya.

Mai taimakawa ministar Kuɗi a ɓangaren yaɗa labarai, Yunusa Abdullahi, ya ce a tuntuɓi CBN ko kuma gwamnan da ya yi zancen.

A wani labarin kuma EFCC ta bayyana dalilin da yasa take Amfani da Otal ɗin da aka ƙwace a hannun Dasuƙi

Hukumar dake yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta bayyana dalilin da yasa take amfani da Otal ɗin da aka kwace a hannun Sambo Dasuƙi.

Shugaban EFCC reshen jihar Kaduna ya ce jami'an su na amfani da wurin ne na ɗan wani lokaci musamman waɗanda aka canza ma wurin aiki zuwa Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262